Kishin addini babu ilimi, yana da hadarin gaske.

 Kishin addini babu ilimi, yana da hadarin gaske.





Akwai wata rana na je Niger road, cikin Sabon Gari, Kano; wajen masu printing. Wani mutum Musulmi ya bawa wani mai aikin printing 'Kirista' printing na wani 'receipt' irin na hayar shago, to a jikin 'reciept' din, akwai rubutun 'ajami' (Hausar Larabci) na sunan mai shagunan "الحاج...." a sama (heading).


Bayan kammala 'printing' sai wannan mai aiki ya tattare aiki ya ajiye a 'kasa, a gefe, waje guda a jikin bango. Can sai wani mutum ya shigo shagon, yana ganin wadannan 'receipt' da rubutu ajami, sai ya hau daru da hayaniyya; yana rantse-rantse, cewa, "wallahi Musulmai ba za su yarda ba, ya za a yi a kirista ya ajiye Alkur'ani a Kasa?" ya yi ta daru. Shi kuma 'mai aikin printing' (Kirista) ya rikice, mutane har sun fara taruwa.


Can, sai wani mutum (dan) dattijo ya zo, ya ce "me yake faruwa ne?" Mutumin nan cikin bacin rai, ya maida masa bayani. 


Sai dattijon ya dauki "receipt" ya karanta. Sai ya bawa mutumin nan 'mai hayaniyya' ya ce ya karanta. Sai ya sunkuyar da kai (ma'ana, bai ma san me aka rubuta ba). 


Sai dattijon nan Ya ce, "gaskiya baka yiwa kanka da Musulunci adalci ba, baka ma san me aka rubuta ba! Wannan hayaniyyar taka in ta tashi, Allah kadai ya san adadin rayukan da za a rasa (da sunan rikicin addini), ta sanadin aiki da jahilcinka..."


Zafin kai, ba shi ne addini ba. 

Addini ana yinsa da ilimi ne.


✍️ Aliyu M. Ahmad

11th Shawwal, 1443AH

12th May, 2022CE

Post a Comment

1 Comments