Ku Tausayawa Masu Karamin Karfi

Na kan ji kamar na zubda hawaye, idan na ga magidanci ana kokuwar karbar abin shan ruwa da shi a titi. 


Wallahi da gaske, akwai wadanda tun da Ramadhan ya kama; kwanaki 4 kenan, ba a dora tukunya a gidansu ba. Sai abin da aka samu a titi na sadaka. Ba kuma nema ne ba a iya ba. Wasu aikinsun ya yi wahala. 


Wani ya yi aikin wahala: aikin barema, leburanci ko birkilanci, ba a biya shi hakkinsa ba. Wasu kuwa sana'arsu bata iyuwa da azumi; kuma da ita suka dogara suke dawainiyyar rayuwarsu. Rayuwar ba duk aka zama daya ba. 


Wani bai iya roko ba, ba zai iya zuwa ya fada ma matsalarsa ba, balle ya ce ka taimake shi. 


Don Allah! Ka taimakawa wanda na kusa da kai, da abin da zaka iya.  Wani #500 a wajensa, tamkar 50k take; don zata biya masa bukatar kashe yunwar cikinsa. 


Ka yi kokarin yayewa bayin Allah kunci da takaici, kai ma Allah Ya ye maka naka kunci a duniya da lahira, ya kuma biya ma bukatunka na alheri. 


Barkanmu da shan ruwa! 

Allah Ya amsa mana baki daya.


Aliyu M. Ahmad

04-09-1443AH

05-04-2022CE


Photo Credit: UNICEF (Connect) Photographs


Post a Comment

0 Comments