#Ramadaniyyat 009
Duk mai bawa Allah zabi a cikin al'amuransa baya taba da-na-sani a rayuwarsa.
In ka tashi addu'a, ka roko Allah ya baka mafi alherin rayuwa, na abin da zai zama maslaha ga addininka da kuma karan kanka.
Ka roki Ubangiji ya baka mafi alherin aboki/abokiyar zama, aiki, dukiya, jin dadin rayuwa... kada ka kwallafawa ranka dole abin da kake so sai ka mallake shi.
Domin sau da yawa abin da muke so, sharri ne ga rayuwarmu, ba mu sani ba; wani abin da muke 'qi' kuma alheri ne a gare mu ba mu sani (Baqara, aya ta 216).
Shi ya sa Nana Aisha رضي الله عنها tace: "Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya koyar da ita wannan addu'ar:
اللهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ مِنَ الْخَيْرِ كُلِّهِ عَاجِلِهِ وَآجِلِهِ، مَا عَلِمْتُ مِنْهُ وَمَا لَمْ أَعْلَمْ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنَ الشَّرِّ كُلِّهِ، عَاجِلِهِ وَآَجِلِهِ مَا عَلِمْتُ مِنْهُ، وَمَا لَمْ أَعْلَمْ....، وَأَسْأَلُكَ أَنْ تَجْعَلَ كُلَّ قَضَاءٍ تَقْضِيهِ لِي خَيْرًا
[Adab al-Mufrad, 679]
Manzon Allah صلى الله عليه وسلم ya ce: "Allah Ya karbar addu'ar bawa, matukar babu sabo, ko yanke zumunci ko gaggawa a cikin addu'ar" [Sahih Muslim, hadisi na 2736].
Idan ka yi addu'a ka bawa Allah zabi cikin addu'arka, zaka sami dayan uku; ko a amsa ma bukatarka, idan alheri ce, ko Ubangiji ya musanya ma da abin da ya fi abin da roka alheri, ko kuma a ajiye ma ladan ibadar addu'a har ranar Alkiyama [Musnad na Imam Ahmad, 10749].
Allah Ya mana zabin rayuwar da take mafi alheri ce gare mu da kuma ahlinmu, amin.
✍️Aliyu M. Ahmad
9th Ramadan, 1443AH
10th April, 2022CE
0 Comments