KA YI AURE, KA YI AURE




Ka yi aure, ka yi aure, aure IS NOT MERELY 'ka yi aure' fa kawai, don kana samun ‘yan kudaden kashewa, ko ka dan ja shekaru, ko sanya sutura mai dan haske, ko kana soyayyar 'I love you darling...'


Aure ba ana yi don a dauke sha'awar juna ba ne kawai, don kana kana ji da samarta; Aure ya fi nuna symbol (alama) na cikar mutum, wanda ya kuma shirya daukar nauyin wasu mutanen su rayu a duniyar nan, da ya iya gwagwamayar rayuwa kamar haka:


Financially, idan dai asusun ajiyarka a yanzu yana reading ₦0.00 ko; kafin ka dauko maganar aure, ka fara lissafin 3 - 5 millions (lower standard). Kama daga mallakar gida, kayan aure da sauran hidimar auren kansa. Sannan bayan an yi aure shin kana da hanyar neman kudin da za ka ci gaba da rike matar tare da ‘ya’yanku?


A addinance, Shin kana da ilimin hukunce-hukuncen auren? Mene ne matsayin aure a kanka? Wajibi ne a kanka, ko Mustahabi, ko Makruhi, ko ma Haraam. Ka san hakkinka, hakkin matar, hakkin zuri'arku da yanayin zamanku? 


A kimiyyance, kana da lafiyar da zaka iya sauke hakkin aure? Lafiyarka, lafiyarta, ya ‘genotype’ (الطراز العرقى) dinku kai da matar?, Shin baka ko bata da wata cuta da zaku iya cutar da junanku ko zuri’arku?


A zamantakewa, mene ne asalinku? Kai karan kanka kana da tarbiyyar da har zaka iya bawa wasu tarbiyya? Iyayenku sun aminta su kasance tare da wacce kake niyyar ku zauna tare? Shin ita wacce kake nema da aure ta amince ku kasance tare? 


Gaskiya a takaice ma, in baka shiryawa aure ba, kar ka batawa kanka da ‘yar mutane lokaci, kar ka yarda mutane su maka turin mutuwa, ka yi aure, ka yi aure, bayan aure ba mai ma ‘cefene’; KAWAI KA TAFI NEMAN DALILIN da zai tabbatar ma ka yi nasara wajen aure. 


Ka duba ‘Raudatul Muhibbin’ na Ibn Ibn Qayyim Al-Jawziyyah, ‘Fiqhul Hub’ na Sheikh Birjas, ‘Rifqan Bi-alqawarir’ na Al-Jibaly domin neman Karin bayani a takaice.   


Allah Ya hore mana daga falalarsa 🤲🏻


© Aliyu M. Ahmad

24th Sha’aban, 1443AH

27th March, 2022CE

Post a Comment

0 Comments