Social media ta zo da alkhairai masu yawa, amma ta wata fuskar kuma, akwai sharri shi ma mai yawa. Daga cikin illolin 'social media' akwai yaduwar alfasha. Kallon 'bat*a' (po*n) a media ya shafi mutane da dama, sai wanda Allah ya tseratar [Yusuf, aya ta 53].
Shawarar da zan bawa ma'aboci kallon alfasha (ba*a/po*n) a yanar gizo:
1. Kai tsaye, kallon hotuna, bidiyo ko karanta wallafar dake tayar da hankali a 'media' haramun ne. Umarni ne daga Ubangiji ﷻ, cewa; "a fadawa mummunai maza da mata, su rika runtse idanuwasu, su kuma kiyaye al'aurarsu" [AnNur, aya ta 30].
2. Duk aiyukan da gabban jikinka suka aikatawa, da 'ji' da 'gani' da abin da zuciya ke kullawa, za a tuhume ka akansu, a ranar Alkiyama [Al-Isra', aya ta 36].
3. Kallo bat*a (po*n) yana da wuyar dainawa idan ya zamewa mutum jiki (addiction), har ga masu aure; saboda fitina ce. Shi yasa Ubangiji ﷻ ya yi mana gargadi da cewa, "kar mu kusanci zina" [Al-Isra', aya ta 32]. "Kada mu kusanci alfasha, wacce ta bayyana da wacce take a boye..." [Al-Anam, aya ta 151].
4. Kallon bat*a (po*n) ZINA NE. Zina bata takaita a iya haduwar 'namiji' da 'mace' ba; sauran gabban jiki ma suna zina. Zinar ido, ta ce kallon haram (tsiraici/bat*a). Zinar harshe, ita ce zantukan batsa... farji ke gaskata hakan ko ya karyata [Bukhari, 5889].
Kuma, yawaita kallo ko sauraro 'ba*a (po*n), ya kan ja mutum zuwa ga aikata babbar zina, ko istimna'i, dss [Sahih Muslim, 2657].
5. Ka ji tsoron Allah ﷻ a duk inda kake. Ko da ka boye/buya a wani waje, ko ka goge 'history' don kar mutane su sani; mu sani, duk abin da muke Allah ﷻ ya sane da abin da muke aikatawa [Jami' al-Tirmidhi, 2115].
6. Idan wayarka zata zame ma fitina, barin amfani da 'social media' din baki daya shi ne yafi ma alheri. Ka yi kokarin kaucewa duk shafukan da suke yadawa alfasha, ta hotuna, bidiyo ko rubutu, ko raye-rayen bat*a. Kallo bat*a masifa ne, koda aure mutum ya yi, yana da wuya ya daina, matukar ya zame masa jiki (addicted).
Allah Ya tsare mu daga afwaka zina ta kowacce fuska; gani, ji... Allah Ya shiryar mana da zuri'a.
✍️ Aliyu M. Ahmad
9th Shawwal, 1443AH
10th May, 2022CE
0 Comments