BAHAUSHE DA SOYAYYAR MANZON ALLAH ﷺ

 BAHAUSHE DA SOYAYYAR MANZON ALLAH ﷺ

 
A gidan Bahaushe ne saboda soyayyarsa da Manzon Rahama ﷺ da iyalan gidansa zaka samu ya sanyawa duk 'ya'yansa suna 'Muhammad'. In kuma aka haifa masa tagwaye (twins) ya sa musu sunan Hassan da Hussaini kai-tsaye (automatic).

Duk da Bahaushe yana sunayen Hausawa, na ranaku (Dan Jummai , Danladi, Talatu, Ladi ...) ko yanayi da lokaci (Shekarau, Damina...) ko siffa (Sadauki, Jarumi, Maikudi...)... Gambo, Gagare, Auta da sauransu; amma tasirin addini ya sa aka sauya, ake dauko sunan Larabawan Sahabbai da Iyalan Manzon Allah ﷺ, ba don sunayen Hausawan ba su da kyau ba, a'a tasirin addini ne.

Ko cikin sunayen mata, zai yi wuya ka samu gidan da babu mai sunan diyar Manzon Rahama ﷺ, Nana Fatima ko Rukayya ko sunayen iyayen mummunai Nana Khadija, ko Aisha, ko Hafsat, ko Saudat, ko Zainab, ko Safiya, Juwairiyya, Ramla ko Maimuna رضوان الله عليهم.

Ya jikan Marigayi Majidadi Hadejia, Alh. Yahaya Kwatalo. A iya sanina, duk 'ya'yansa maza sunansu 'Muhammad', sai dai ya bambata su da Muhammad Auwal (Lawal/Lawan), Sani, Salisu, Rabi'u ... Hadi Majidadi... da sauransu.

Tasiri da kusancin Annabi ﷺ da Sahabansa رضوان الله عليهم ya sa zai yi wuya ka tsallake gidan Bauhaushe daya, biyu... baka sami mai sunan aminin Manzon Allah ﷺ, Abubakar (Garba ko Habu) ba, ko Umar (Faruku), ko Usman, ko Aliyu (Sadauki) ko Khalifa (bai daya).

Ko ba a ambaci sunan Muhammad kai tsaye ba, zaka ji ana ambatar mutum da inkiyar Manzon Allah ﷺ, Ahmad, Mahmud, Hadi, Rashid, Bashir...

Ko ni a cikin gidanmu, sunan kakanmu Ahmad, sunan mahaifinmu Muhammad. Sunan babban yayanmu Ahmad. Wanda ya biyo ni, sunan Muhammad, dan autanmu shi ma sunansa Muhammad.

Zan iya rantse ma, da ko Larabawa da Habibu ﷺ Ya fito ta tsatsansu, ba za su zarce Bahaushe wajen nuna soyayya da kishin Manzon Rahama ﷺ ba. Ko ta wajen yadda Bahaushe ke lakkabawa 'ya'yansa sunayen Manzon Allah ﷺ, kai tsaye, ko lakabi.

Bahaushe kan soyayyar ma'aiki gagara-badau ne. Babu zancen tsagi ko bangaranci, Kowa na Ma'aiki ﷺ ne.

Allah Ya kara mana soyayyar Abin Kauna ﷺ, da iyalan gidanSa da Sahabbansa رضوان الله عليهم, da bin tafarkinsa cikin aiki da magana, amin.

✍️ Aliyu M. Ahmad
13th Shawwal, 1443AH
14th May, 2022CE

Post a Comment

0 Comments