Tambayi kanka❗
Ya za ka kalli wani ɗan uwanka ko abokinka, a kullum ya tashi da safiya sai ya ɗauki wuƙa ko wani abu mai tsini na cutarwa; ya sokawa kansa, ya yi wa kansa rauni? Har wajen yana jini, yana jin zafi? Ko kuma wani ne ke soka masa wuƙar, yana yi masa rauni, kana gani.
Wannan abin da ya ke a zahiri kenan (physiological), rauni ko cuta da muke iya gani da idonmu. Za mu ce, wane yana cutar da kansa ko ana cutar da shi. Mu kan ɗauka, cuta ko jinya ita ce (kaɗai) abin da muke (iya) kalla a zahiri (physical), bal; cutarwa ta cikin kwakwalwa da tunani (emotional/psychological) ta fi ta zahiri muni.
Kamar haka yake mu'amala da wasu mutanen, psychologically kana cutar da kanka, a kullum ba ka da wata riba a alaƙarka da su face cutuwa, ƙunci a zuci, fargaba, faɗuwar gaba...
Matakin farko a falsafar likitanci na warkewa daga cuta shi ne, gujewa musabbin cutar in ji Hippocrates na Turawa, Thomas Sydenhan (1624 - 1689). Wannan shi ne ake ƙira da "PREVENTIVE MEDICINE". Yake cewa, “the first step in healing is to remove the cause of the disease".
Wannan abun cutarwa kuwa, abinci ne da kake ci ko abin sha yake sanya maka jinya? Ko wani abu ne kake kallo da idonka yake sanyawa idonka ciwo? Ko wani mutum ne (saurayi ko budurwa, mata ko miji, aboki ko wani abokin zama) suke ɗaga maka hankali? Dole ka haƙura da su, domin kuɓutar da kanka daga
cuta. Ubangiji ﷻ yana cewa, "ولا تلقوا بايديكم الى التهلكة"
Duk soyayyarka ko ƙaunarka da wasu mutane, dole ka haƙura da su saboda cutar da kai suke yi, ko kana cutar da kanka saboda kwallafa rai a kansu. Ba za ka taɓa rabuwa da fargaba da ɓacin rai ba har sai ka sallame su (psychologically) daga rayuwarka, ka haƙura da su, a kowane mataki ne kuwa, soyayya ta saurayi da budurwa, ko a zaman aure; ga mace ko namiji. Shi ya sa Shari'a ta halasta saki (talaƙ) ga miji ya sawwaƙewa matarsa, ko matar ta nemi khul' domin samun maslaha.
Hippocrates (c. 460 - 370 BC) yake cewa, "if you are not your own doctor, you are a fool". Ma'ana, "idan ba kai ne likitan kanka ba, kai wawa ne". Ire-iren cutattuka da suka shafi irin wannan 'distresses', ba wani magani, ko shawara da maganganu da za su yi maka tasirin kuɓutar da kai, fa ce kai a karan kanka ka yi wani huɓɓasa. Za ka ci gaba da komawa ne, ana cutar da kai, kana cutar da kanka (repetition compulsion).
*NB: A kullum ka tuna! Kai ke da alhakin abubuwa da yawa a rayuwarka, ciki har da zaɓawa kanka cuta ko amfani. Abin da ya fi ƙarfinka shi ne ƙaddara ba yadda za ka iya, sai haƙuri.
✍️Aliyu M. Ahmad
4th August, 2025 CE
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliyuCares #AliMotives
0 Comments