Matakin farko da za ka sauƙaƙawa kanka rayuwa shi ne, KA SAN KANKA, ka kuma rayuwa daidai da matsayinka a kowanne mataki na rayuwa.
Rashin sanin kai ya sa muke wahalar da kanmu a abubuwan rayuwa da yawa, ni na san matakin tattalin arziƙina da na iyayena, ba zan yi hanƙoron rayuwar irin ta wanda ya fi ni arziƙi ba, haka nan ba zan ƙasƙantar da wanda yake ƙasa da ni ba. Yadda nake hango wani a sama, haka wani yake min wannan hangen. Kamar yadda zan kalli wani ƙasa da ni, wani ko kallon ma ban ishe shi ba.
Misali, ta fuskar tattali; ba abin mamaki ba ne, wanda yake ɗaukar salaryn ₦750k a wata, ka ji yana cewa kuɗin albashinsa ba ya isarsa a wata, kamar yadda mai ɗauka ₦100k shi ma yake ƙoƙarfi. Su buƙatun rayuwa suna tafiya ne da yawan kuɗin da kake tsammanin za su shigo ma. Don wani ya ce, ₦500k ce za ta iya riƙe masa gida, da 'ya'ya 2, hala salarynsa ₦250k - ₦350k ne, ba ya wadatar da shi bisa doron buƙatunsa na yau-da-kullum, shi ma bai kamata ya yi judging wanda yake rayuwa cikin aminci da ₦150k a wata ba.
Zuwa Shoprite, ko wani sananne joint ko restaurant a Kano, shi ne abin da za ka iya affording, ka yi nishaɗi, ka ɗauki hotuna, ka watsawa duniya. Wani kuwa ya fi ƙarfin zuwa waɗannan wuraren, ƙasashen waje yake zuwa, Dubai da Paris, irin abin dai da waɗanda suka je Shoprite da gidan Zoo, ɗaukar hoto, nishaɗi, cin abinci... shi ma haka zai yi, ba bambanci, sai bambancin dama da kuma muhalli (kowa yana yin abin da zai iya ne).
Muna shiga cikin mutane, a taruka da dama. Mutumin da ake rububin yin hoto da shi a wani taron, saboda shi ne star, shi ma gaggawa yake ya yi hoto da wasu a wani taron, saboda akwai taurari da suka haska sama da shi.
Idan 'yan siyasa suka ba wa wani ₦10k a shekara don ya kare muradinsu, wani ₦100k za a ba shi, wani kuwa ya fi ƙarfi ₦1 million ma, kowa da farashinsa, kuma yana karɓa ne daidai da matsayinsa.
Akwai wanda yake cewa, shi ba wani ɗa siyasa da zai sama masa aiki (offer), ya zo yana hoto da shi ana yaɗawa, hala yana ga ya fi ƙarfin haka (shi a karan kansa), amma shi a social media aka ba shi offer, yana sharing tare da abokansa suna taya shi murna. Rayuwar nan fa, ka san matsayinka ne, kuma kada ka kwatanta kanka da wasu, na sama ko na ƙasa da kai. Manifar ita ce, kowa ya yi arriving a abin da yake son cimma a rayuwa (aiki, gina kai, mallakar wani abu...).
Mota ce za ka siya ƙure asusunka, ka siya ta ₦12 million, wani kuwa yanzu-yanzu ya yi cinikin motar ₦150 million, kamar yadda wani a tattalin arziƙinsa da buƙatarsa, babur zai iya siya na ₦500k.
Social media ta haɗa mutane da dama, masu bambace-bambance a kowanne matakin rayuwa. Ka san kanka, kada stressing kanka da irin rayuwar kowa, ka yi rayuwa daidai da ƙarfinka ta kowacce fuska.
Bissalam!
✍️Aliyu M. Ahmad
25th July, 2025 CE
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliyuCares #AliMotives
0 Comments