Wani lokaci, Facebook kan iya bankaɗo post da ka yi shekara 5 baya, idan ya saɓa da wani policy da aka ƙirƙira a yau, kuma su ɗauki mataki a kansa.
Misali spams, ko counterfeit, za su goge su kuma yi maka gargaɗi, ba wani abu ba ne.
Ka jira za su cire maka da kansu.
Akwai categories na profile status 🟩, 🟨 da 🟥
🟩 Kore (green) - Good Standing, na nufin profile naka ƙalau yake, ba shi da 'issue' na komai.
🟨 Yellow kuma, WARNING ⚠️ gargaɗi ne, bayan sun detecting spams a kan shafinka, ko wani post da ya saɓa da wani policy na yau, za su goge ne, su kuma bar maka alamar 🟡 (gargaɗi), ba komai ba ne.
🟥 Ja (red), shi ne mai matsala, idan an same ka da ɗora graphic contents, ko wani content da yake tada hankali (graphic/sensitive content), ko copyright infringment, ko an reporting naka da jin zarafi (harrasment report) da sauransu.
Restrictions kuma kala-kala ne, akwai partial, kamar su hana ka comments ko posting na ɗan wani lokaci, ko 'shadow blind/ban' (su hana post naka tafiya sosai 'low reach') ko kuma su yi maka barazanar goge maka account, ko ma a rufe shi ba ki ɗaya (full restrictions).
Ba wata 'criterion' ta cire 'issue' ko 'restrictions' da wai za a yi ta mentioning sunanka za su cire maka, a'a; idan ka sami issue ka yi appealing ta 'dialogue box'. Idan ka tura ma, zai iya yin shekara ba su cire ba, wannan ba ya nufin kana da issue matuƙar gargaɗi ne 🟡, ba wani hukunci suka ɗauka ko wani abu (kamar hana ka chats ta Messenger, posting da comments) shafinka ya daina yi ba.
Wani lokacin, shi kansa yawan ambatar sunanka zai iya zama illa, 'spams', ko ya samar maka da 'coordinated harm'. Facebook ba mutum ba ne, 'algorithm' ne, da zarar ya detecting abin da aka tsara masa take zai yanke hukunci.
✍️Aliyu M. Ahmad
8th August, 2025
#AliyuCares #RayuwaDaNazari #AliyuMAhmad
0 Comments