Kada Ka Cire Albarka Ilimi a Rayuwarka


Wani CONTROVERSY da matasa ke ganin kamar cinyewa ne, alhalin tunkuɗe albarka suke a rayuwarsu:

Sai ka ji mutum yana cewa:

"Ba wanda ya koya min wannan skill. Ni na koya da kaina, daga YouTube ko hanyar amfani da AI".

Su waɗanda ke koyarwa a YouTube ba malamai ba ne? Shin self-taught yana nufin babu wanda ya ba ka wahayi ko ya taimaka maka kai tsaye ko a fakaice? Ko instructions ka karanta na wani abu, karatu ne, kuma wani ne ya rubuta, kuma ilimi ne.

Nothing found in a vacuum, sai dai idan wahayi ake yi maka, but you must learn something somewhere from someone. Komai da kake iya yi, akwai wanda ka gani, ka saurara, ko ka karanta daga gare shi. Babu wani skill da mutum zai koya a vacuum sai dai idan ana yi masa wahayi ne daga sama (shi ma koyarwa ne).

Ba kai ka koya wa kanka komai ba, ko da ka koya daga bidiyo, karatu, ko kallo, ko da inspiration ne ma ka samu daga wani, ka girmama ilimi.

Yin iƙirarin cewa "I am self-made" ko "Nobody taught me" wani lokaci na nuna raina ƙoƙarin wasu, musamman waɗanda suka ba da lokaci ko iliminsu ta hanya kai tsaye ko ta hanyar da baka sani ba. Kada mu rage darajar gudummawar wasu a rayuwarmu. Babu wanda ya zama wani abu ba tare da wani ba.

Sayyidina Aliyu (RA) yana cewa:

من علمني حرفًا، صرت له عبدًا

"Duk wanda ya koya min harafi guda (koda alif ce), to na zama bawansa"

Wannan yana nuni da cewa ilimi yana da daraja sosai, kuma wanda ya koyar da kai wani abu yana da matsayi mai girma a rayuwarka. Kada ka raina wanda ya koyar da kai, ko da abu kaɗan ne.

Ilimi yana da daraja, kuma malamai su ne tushensa. “Self-taught” ba yana nufin ka koya komai da kanka bane ko da a kafofin zamani ne, akwai wani da ya saka maka hannu, shi ma na YouTube ko AI, masu koyarwa ne, malamanka ne.

A tarihin ilimi da kwarewa, ba a taɓa wani kwararre da wai shi ya gina kansa ba, dole yana da malami da kuma waɗanda suka yi tasiri a rayuwarsa. Ɗaya daga cikin rashin albarka ilimi ma shi ne, ka ɗauka ka isarwa kanka, kai mutum mai rauni. Kada ka cirewa kanka albarka da kanka!

✍️Aliyu M. Ahmad
11th Muharram, 1447 AH
6th July, 2025 CE

#RayuwaDaNazari
#AliyuMAhmad
#AliyuCares

Post a Comment

0 Comments