Sujjadar mantuwa/rafkanuwa (sahwu) a cikin sallah sunnah ce. Saboda hadisin Ibn Mas’ud رضي الله عنه Manzon Allah ﷺ Ya ce: “إذا نسي أحدكم فليسجد سجدتين” Ma’ana "idan ɗayanku ya yi rafkanuwa a sallah, ya yi sujjadu guda biyu" (Muslim, 402).
• A cikin hadisin Dhul-Yadaini, Annabi ﷺ Ya yi sallah tare da sahabbai رضوان الله علبهم da maraice (Azahar/La’asar), Ya sallace ta da raka’a biyu, ya yi sallama. Har Manzon ﷺ Allah Ya tashi ya zauna kan wani itace, sai wannan mutumin ya tambayi Manzon Allah ﷺ a game da rage sallah. Shugaba ﷺ Ya tambayi sahabbai kan abin da Dhul-Yadhain ke magana a kai, suka amsa da cewa, EH! AI AN RAGE SALLAH. Sai Manzon Allah ﷺ Ya yi kabbara ya cike raka’o’in da Ya bari, ya yi sujjada guda 2 (BA’ADI), Ya sallame ﷺ (Bukhari, 482).
• A (wata) ruwayar ta Abdullahi bin Buhainatu رضي الله عنه, Annabi ﷺ Ya sallaci SALLAR AZHAR tare da sahabbai رضوان الله علبهم, sai ya wuce bai yi TAHIYA TA FARKO ba. Bayan ya yi TAHIYAR ƘARSHE, sai ya sake KABBARA, ya yi sujjada (ƘABLI), ya sallame ﷺ (Muslim, 573).
• Ibn Mas’ud رضي الله عنه ya ce: Manzon Allah ﷺ Ya yi sallar Azhar raka’a 5, sai sahabbai suka tambaye shi “shin ko an ƙara sallah ne?” Sai ya yi SUJJADA 2 bayan sallah [BA’ADI] (Muslim, 572.)
Ana yin sujjadu guda biyu (2) ne idan aka samu ƘARI, ko RAGI (ko kuma ƘARI da RAGI a lokaci guda) ko SHAKKA a cikin sallah.
Waɗannan sujjadun ana yin su kafin a sallame (ƘABLI) ko bayan an sallame sallah (BA’ADI), a Mazhabar Malikiyya.
Duba da fiƙhun sauran Mazhabobi, Misali, a HANAFIYYA ‘ba’adi’ kawai a ke yi, a SHAFI’IYYA kuma ‘ƙabli’ ce kawai idan an yi rafkanuwa. Mazhabar Malikiyya ce a mas’alar ‘sahwi’ ta fi inganci, kuma an fayyace bayanin SAHWU dalla-dalla a taƙaice cikin LITTAFIN AKHDARI.
======================
* Littafin AHLARI an rubuta shi a bisa fahimtar Mazhabar Malikiyya ta Imam Malin ibn Anas رحمه الله, haka ma wannan RUBUTUN.
======================
Kafin mai sallah (Musulmi) ya fahimci yadda zai gyara sallarsa da “sujudus sahwi” yana da kyau ya san sharaɗai, rukunai, farillai, sunnoni da mustaban sallah.
Saboda:
• Akwai aiyukan da rage su ko ƙara su na sa a yi “sujudus sahwi”.
• Akwai aiyukan da barin su ba ya sa a yi sujjada.
• Akwai kuma aiyukan da sai sun kai wani adadi za a musu sujjada.
• Akwai aiyukan da barin su (kaɗai) ɓata sallah suke baki ɗaya.
• Akwai aiyukan da barin su yana ɓata raka’a kaɗai, sai a zare ta, a jefar, a sake ta, sannan a yi sujjada.
---------------------------------------------------
YADDA AKE SUJUDUS SAHWI
---------------------------------------------------
• Wanda ya yi RAGIN WANI AIKI a cikin sallah ZAI YI ƘABLI (sujjada kafin sallama).
• Wanda ya yi ƘARI a cikin sallah, ZAI YI BA’ADI (sujjada bayan sallama).
• Wanda ya yi SHAKKA a cikin sallah, zai yi gini akan yaƙini.
MISALAI:
------------------------------------------------------------
RAFKANUWAR DA AKE YI WA ƘABLI
------------------------------------------------------------
𝟭. ƁOYE KARATUN SALLAH A SALLAH A WAJEN BAYYANAWA. Wanda ya tuna kafin ya tafi ruku’u, zai dawo ya sake karatun a bayyane. Idan iya KARATUN SURAH ne, babu sujjada a kansa (idan ya dawo ya sake karatun). Idan kuma ya ƙulla raka’a (yin ruku’i) zai yi ƘABLI.
Idan kuma FATIHA ce ya ɓoye a wurin bayyanawa, zai dawo ya sake a bayyane, ya kuma yi BA’ADI.
2. Tsallake aya ɗaya cikin karatun Fatiha (za a yi ƘABLI). Idan kuma ya wuce aya ɗaya, sallah ta ɓaci.
Idan kuma a karatun surah ne, mutum ya cije, zai tsallake ya je ta gabanta, idan babu mai tuna masa, zai wuce ya yi ruku’u, BABU KOMAI A KANSA.
3. Rage sunnah 2 zuwa sama.
4. Ba za a yi sujjada ƘABLI saboda rage Ruku’u, ko karatun Fatiha, ko Sujjada.
Wanda ya manta karatun fatiha, RUKU’U, ko SUJJADA a cikin sallah, zai dawo ya rama su, sannan ya yi sujjada BA’ADI. (*Bayaninsu yana ƙasa).
5. Wanda ya manta tahiyar farko, zai yi ƘABLI.
--------------------------------------------------------------
RAFKANUWAR DA AKE YI WA BA’ADI
--------------------------------------------------------------
1. ƘARA RAKA’A. Misali, wanda ya tashi ƙarin raka’a ta 3 a sallar Asubah, ko raka’a ta 4 a sallar Magriba, ko raka’a ta 5 a sallolin Azahar, La’asar ko Isha’i. Idan ya tuna bayan ya tashi, zai dawo ya zauna, sai ya yi sujjada bayan sallama (BA’ADI).
2. Bayyana karatun sallah a wajen ɓoyewa.
3. Kokwanto tauye raka’a za a cika, sannan a yi BA’ADI.
4. Karanta wani harafi da bana cikin Alƙur’ani ba, ko canja harafan Alƙur’ani.
5. RAGE RUKUNI. Misali, wanda ya manta KARATUN FATIHA, ko RUKU’U, ko SUJJADA, zai jefar da raka’ar, ya gina wata, sannan ya yi SUJJADA BA’ADI.
6. Wanda ya manta sujjada ta 2 a raka’ar farko, bayan ya tashi daga ruku’un raka’a ta biyu, sai ya tuna bai yi sujjada ta biyu ba a raka’a ta farko, to, zai koma ya zauna ya yi sujjadar, sannan ya cika sallarsa, ya yi sujjada BA’ADI (ita kuma waccar raka’a ta 2 a jefarta).
7. Wanda ya maimata karatun Fatiha da rafkanuwa zai yi BA’ADI. Idan kuma da ganganci ne, SALLAH TA ƁACI.
-------------------------------------------------------------------------------
RAFKANUWAR DA BA A YI WA ƘABLI DA BA’ADI
-------------------------------------------------------------------------------
1. Tauye sunnah guda ɗaya (sai an tauye fiye da ɗaya ne ake yin ƘABLI), amma banda sunnar bayyanawa ko asirta karatu.
2. Wanda ya manta mustahabbi, babu sujjada a kansa.
---------------------------------------------
* Misalan Mustahabban sallah su ne:
• Ɗaga hannaye yayin kabbarar harama,
• Faɗin رَبَّنَا وَلَكَ الْحَمْدُ bayan ɗagowa daga ruku’u,
• Tasbihi cikin ruku’u,
• Damanta sallama,
• Motsa ɗan yatsa (sabbaba) a tahiya… da sauransu.
---------------------------------------------
3. Tuna rashin bayyanawa ko asirtawa na karatun surah (banda Fatiha) kafin tafiya ruku’a idan mai sallah ya dawo, ya sake karatun a bayyane ko a ɓoye, BABU SUJJADA A KANSA.
Idan kuma ya wuce zuwa ruku’u, sai ya yi BA’ADI saboda ɓoyewa (a inda ake bayyana karatu), ko ƘABLI (saboda bayyana karatu a inda ake asirtawa).
4. Wanda ya je tashi a zaman sujjadar farko, zai dawo ya zauna kafin hannayensa su rabu da ƙasa, to zai dawo ya zauna, BABU SUJJADA A KANSA.
Amma idan hannayensa sun bar ƙasa, zai miƙe ya ci gaba da sallah, sai ya yi KABLI.
Idan kuma ya dawo, bayan ya rabu da kasa, a rafkane ko a sane, zai yi sujjada BA’ADI.
5. Furta zance kaɗan (idan ba da ganganci ba ne).
6. Nuni da hannu, ko kai, matuƙar jiki bai juyawa Alƙibla baya ba.
7. Waiwaye a sallah bisa mantuwa, babu komai a kansa. Idan da ganganci ne ya yi MAKHURI, idan kuma waiwayen ya sa gangar jikinsa juyawa, sallarsa ta ɓaci, SAI YA SAKE.
8. Gatsa, ko amai, ko ajiyar numfashi ko nishi (saboda da ciwo) na marar lafiya (bada ganganci ba).
9. Yin kuka domin tsoron Allah.
10. Yin shiru (dan kadan) saboda sauraron magana.
11. Atishawa cikin sallah. Kuma ba sai mutum ya yi HAMDALA ba, haka nan ba zai mayar da YAHDIKUMULLAH ga wanda ya ce masa: YARHAMUKALLAH. Idan kuma ya faɗi (Alhamdulillah), babu komai a kansa.
12. Wanda ya yi gyangyaɗi (kaɗan) a cikin sallah BABU KOMAI A KANSA. Amma idan ya yi nauyi, zai sake alola, ya kuma sake sallah.
13. Ƙarin karatun surori a raka’a ta 3 ta Magriba, ko raka’a ta 3 da 4 a Azahar, La’asar da Isha’i.
------------------------------------------------------------
RAFKANUWAR DAKE ƁATA RAKA’A
------------------------------------------------------------
1. Manta rukuni. Misali:
• KARATUN FATIHA: wanda ya manta KARATUN FATIHA a raka’a ta farko, har ya ƙulla raka’a ta biyu, zai jefar da waccar raka’a ta farkon, ya maye ta da ta biyu, ya yi BA’ADI.
• RUKU’U: wanda ya manta RUKU’U a raka’a ta farko, har ya ƙulla raka’a ta biyu, zai jefar da waccar raka’a ta farkon, ya maye ta da ta biyu, ya yi BA’ADI.
Idan kuma ya tafi sujjada, sai ya manta bai yi ruku’u ba, sai ya koma ya sake ruku’u ya ci gaba da sallah (amma an so ya maimaita karatun sallah kadan), sai kuma ya yi BA’ADI.
• SUJJADA: wanda ya manta sujjada ta biyu, har ya tashi, bayan ya ƙulla wata raka’ar (ruku’a), zai dawo ya cika ta, sai ya cika sauran sallar, ya yi BA’ADI.
-------------------------------------------------------------------------------
RAFKANUWAR DAKE ƁATA SALLAH BAKI ƊAYA
-------------------------------------------------------------------------------
1. MANTA KABBARAR HARAMA
Wanda ya ƙulla raka’a ko ya sallame, sai ya tuna bai yi kabbarar harama ba, zai sake niyya, ya yi kabbara, ya sake sallah.
2. Yin amai da gangan
3. Nishi da ƙarfi don isar da saƙo (ko da mai sallar marar lafiya ne).
4. Juyawa alƙibla baya
5. Baiyana tsiraici (cikin sallah).
6. Yin Magana ko dariya da gangan (cikin sallah).
7. Yin Salati ga Annabi idan ka ji an amƁACI sunansa, alhalin kana cikin sallah.
---------------------------------------------------
RAFKANUWA TARE DA LIMAN
---------------------------------------------------
1. Idan liman ya yi rafkanuwa a cikin sallah, ya halatta mamu (masu bin sa sallah) su ce masa: SUBHANALLAH, domin ankarar da shi.
2. Liman yana ɗauke rafkanuwar mamu. Sai da:
• Idan ya tauye farilla ne, ko
• Rafkanuwar ta samu mamu yana masbuki (mai cika sallah) rafkanuwar ta same shi.
Misali, wanda aka matse a sahu, ya kasa ruku’u har liman ya ɗago, ya tafi sujjada. Idan mamu zai iya riskar liman a sujjada ta 2, to sai ya yi ruku’un ya riske shi a sujjada ta 2. Idan kuma ba zai iya samun liman a sujjada ta 2 ba, sai ya jefar da raka’ar, ya rama ta bayan liman ya sallame BABU SUJJADA A KANSA.
Idan kuma a sujjada ne aka matse mamu, sai ya yi ƙoƙarin yin sujjadar da bai yi da liman ba kafin liman ya ƙulla wata raka’ar (ruku’u). Idan har liman ya kai ga yin ruku’u na wata raka’ar, nan ma mamu zai jefar da raka’ar, ya rama ta bayan liman ya sallame SHI MA BABU SUJJADA A KANSA.
3. Rafkanuwar liman na hawa kan mamu, matuƙar mamu ya sami raka’a (ko da ɗaya ce) tare da liman.
4. Idan mamu ya sami ƙasa da raka’a ɗaya a tare da liman, ba zai yi sujjadar ƘABLI 𝗸𝗼 BA’ADI ba. Idan ko ya yi, to SALLARSA TA ƁACI.
5. Idan mamu ya samu raka'a ɗaya cikakkakiya ko fiye tare da liman, zai yi sujjadar ƘABLI tare da liman.
Idan kuma BA’ADI ce, zai yi ta bayan ya cika sallarsa. Idan kuma ya yi ba’adi (da ganganci) tare da liman, Sallarsa Ta Ɓaci, idan da mantuwa ne, zai yi BA’ADI.
6. Idan kana bin liman, ya miƙe daga raka’o’i biyu, maimakon ya yi tahiya, za ka yi masa TASBIHI, idan ya rabu da ƙasa, sai ka tashi ka bi shi.
7. Idan liman ya zauna a raka’a ta 1 ko 2 ko ta 3 (a sallar Azahar, La’asar ko Isha’i), kar ka zauna tare da shi (ka miƙe), ka yi masa TASBIHI. Sai ya tashi ku ci gaba da sallah,
8. Idan liman ya yi sujjada ɗaya, ya tashi, kar ka tashi tare da shi, ka yi masa TASBIHI, sai in ka ji tsoron zai ƙulla raka’a, sai ka tashi ka bi shi.
9. Idan liman ya yi sujjada ta uku (3), ka yi masa TASBIHI, KAR KA BI SHI (kar ka yi sujjada ta 3 tare da shi).
10. Idan liman ya tashi ƙarin raka’a ta 5, KAR KA BI SHI, idan kana da yaƙinin ƙari zai yi. Idan kuma ka bi shi (bayan kana da yaƙinin ƙari ce), SALLARKA TA ƁACI.
11. Idan liman ya yi sallama kafin cikar sallar (misali da raka’a), sai ka masa TASBIHI, ya dawo ku cika sallah, ku yi ba’adi.
12. Ana iya gyarawa liman karatu idan ya cije.
* Wanda ya gyarawa wanda ba limaminsa ba karatu, sallarsa ta ɓaci.
13. Ba a gyarawa liman karatu sai an jira (ya yi shiru).
14. Idan sujjada BA’ADI ta kama masbuki ta bangaren limaminsa, shi kuma a lokacin ciko sallah ƘABLI ta kama shi, sai ya yi sujjada ƘABLI ta isar masa.
------------------------------------------------------
RAFKANUWA A SALLAR NAFILA
------------------------------------------------------
Ana yin ‘sujudus sahwi' a sallar nafila, kamar yadda ake yin ta a farilla, sai dai a rafkanuwa cikin karatun Fatiha, karatun surah, asirtawa, bayyanawa, ƙarin raka’a ko manta rukuni cikin rukunan sallah (sujjada ko ruku’u).
1. Wanda ya manta karatun Fatiha a sallar nafilah bayan ya yi ruku’u, zai wuce, sai ya yi ƘABLI.
2. Wanda kuma ya manta KARATUN SURAH a sallar nafila, ko asirtawa, ko bayyanawa, to ya wuce. BABU SUJJADA A KANSA (a sallar nafilah).
3. Wanda ya miƙe domin raka’a ta 3 cikin sallar nafila, ya dawo ya zauna, sai ya yi sujjada BA’ADI. Idan kuma har ya ƙulla raka’a, sai ya cika ta, ya ƙara ta zama 4, sai ya yi ƘABALI.
4. Wanda kuma ya manta rukuni kamar ‘ruku’u’ ko 'sujjada' har ya yi sallama (a sallar nafila), BABU SUJJADA A KANSA.
5. Wanda yake kokwanto a cikin sallar SHAFA’I DA WUTURI, ma’ana, yana tunanin Shafa’i yake, ko Wuturi, ko ya bar raka’ar a matsayin raka’a ta biyu ta Shafa’i, idan ya sallame (Shafa’in), sai ya yi WUTURI.
6. Wanda ya katsar da sallar nafila da ganga, ko ya bar wani rukuninta da gangan, a Malikiyya, sai ya maimaita wannan sallar.
---------------
SHAKKA
---------------
1. Wanda ya yi shakkar cikar sallarsa, zai yi gini a akan bin da yake da yaƙini. Misali, yana kokwanton ya yi raka’a 2 ne, ko 1, to zai yi gini bisa mafi ƙaranci (raka’a 1), sai ya cika 1, sai ya yi sujjadar BA’ADI.
2. Duk wanda ya yi sallama, alhalin yana shakkar a kan cikar sallarsa, to SALLARSA TA ƁACI. Sai ya sake.
3. Wanda ya yi shakka yin sallama a sallah, idan yana kusa, kuma yana da alola, sai ya yi sallamar. Idan kuma ya yi nisa, sallarsa ta ƁACI, SAI YA SAKE SALLAH.
4. Wanda wasi-wasi ya masa yawa, zai zo da abin da yake shakka, sai ya yi sujjada BA’ADI.
5. Wanda ya yi shakka a kan rashin tsarki (misali, yana kokwanton bai yi tsarki ba) ko samuwar najasa (misali fitar tusa, maziyyi, maniyyi ko wadiyyi), kuma ya samu tabƁACIn babu rashin tsarki ko samuwar najasar, BABU KOMAI A KANSA.
Amma idan tunaninsa kan shakkar tsarki ta yi tsayi, to sallarsa ta ɓaci.
---------------------------------------------------
SAURAN MAS’ALOLIN SAHWU
---------------------------------------------------
1. Wanda ya manta sujjada ba’adi, zai rama ta, a duk sanda ya tuna, ko da bayan shekara ne.
2. Wanda ya manta ƘABLI (sujjada kafin sallama) har ya sallame, to ya yi sujjada idan ya kasance yana kusa. Idan ya tsawaita, ko ya fita a masallaci, SUJJADAR TA ƁACI. Sallah kuma tana ɓaci tare ɓacin sujjada (ko a kan sunnoni 3 ne ko fiye da haka). SAI YA SAKE WATA SALLAR.
3. Wanda ya sallame sallarsa kafin ta cika, zai cika sauran, ya yi BA’ADI. Idan kuma ya ɗauki lokaci mai tsayi, zai sake sallar gaba ɗaya.
4. Wanda ƙabli da ba’adi (rafkanuwa 2) suka hau kansa a cikin sallah (ɗaya) zai yi ƘABLI ne kaɗai. Idan kuma ya manta ya sallame, zai yi BA’ADI a take (bayan sallama).
5. Wanda ya manta KABBARORI (ban da kabbarar harama) ko faɗin سمع الله لمن حمده guda biyu ko fiye, zai yi ƘABLI.
6. MAKRUHI ne (abin ƙi) idan kana cikin sallah, wani ya ƙira ka, ka ce masa SUBHANALLAH, don ankarar da shi cewa kana cikin sallah. AMMA SALLARKA TA YI.
7. A Malikiyya, kuskure ne a riƙe Alkur’ani ana dubawa idan ana cikin Sallah, sai dai ga wanda Suratul Fatiha kaɗai ta kakare wa, sai ya buɗe, ya duba. Saboda idan ka mance aya ɗaya cikin Fatiha, babu komai, amma idan ya wuce aya ɗaya, SALLAH TA ƁACI.
8. Wanda wani abun cutarwa ya zo masa alhalin yana cikin sallah (kamar maciji, kunama, cinnaka, wuta…) zai yi ƙoƙarin kare kansa ko ya kashe abun, BABU KOMAI A KANSA. Amma idan motsin ya yi yawa, ko ya juyawa Alƙibla baya, sallarsa ta ƁACI.
9. Wanda ya yi rafkanuwa a lokacin rama wata sallah, daidai yake da wanda yake sallah a lokacinta.
10. A Malikiyya, ana yin TAHIYA bayan ‘sujudus sahwi’ ba’adi ko ƘABLI. Amma za ka iya sallamewa ba sai ka yi tahiya ba (Imam An-Nawawi cikin Sharh Muslim [5/71]).
Allah Shi ne mafi sani.
✍️Aliyu M. Ahmad
22nd Dhul-Hijjah, 1443AH
21st July, 2022CE
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliyusLibray #Karatu #LattafinDonGyaranIbada #Fiqh #Sawh #Sallah

0 Comments