Suratul Kahf


Suratul Kahf

Ita ce sura surar ta '18' cikin jerin surorin Alƙur’ani Maigirma, kuma sura ta '69' da aka sauƙar wa Manzon Allah ﷺ. Ita ce sura da take tsakiyar Alƙur’ani Mai girma (daidai aya ta 74). Makkiyya ce, tana da ayoyi 110, kalmomi 1557, harafai 6360. An sauƙar da ita baki ɗaya (a lokaci guda). Tana daga cikin surori masu darussa da dama da tarin falalar gaske. ‘SUNNAH’ ce karanta a ‘DARE’ ko ‘RANAR JUMA’AH’. 

--------------------------------
DAGA CIKIN FALALAR KARANTA TA:
--------------------------------

1.  “Wanda ya karanta Suratul Kahf a ranar Juma’a za a haskaka masa (sa masa albarka a) tsakanin Juma’a biyu” (Abu Dawud, 4323). 

2. “Duk wanda ya kiyaye ayoyi 10 na farkon Suratul Kahfi a zuciya(rsa) za a kare shi daga (sharrin) Dujjal” (Muslim, 809).

3. “Wanda duk ya karanta Suratul Kahf a ranar Juma’a, haske zai kasance da shi daga duga-dugansa har izuwa giza-gizai dake sama, kuma za a yafe masa zunubansa dake tsakanin Juma’a guda biyu” (Jami'us Sahih, 6470).

* Ana iya fara karanta Suratul Kahf daga daren Juma’a zuwa faɗuwar rana a yammacin Juma’a. Koda mutum bai iya karantawa, ya yi ƙoƙarin sauraro ta sauti (mp3).

--------------------------------
DAGA CIKIN DARUSSAN SURATUL KAHF:
--------------------------------

1. FAƊAR INSHA ALLAH 
(a duk lokacin da mutum ya ƙudurci wani aiki):

Imam Attabary (224 – 310AH) cikin Tafsirinsa (15/142): mushirikan Ƙuraishawa sun aika ‘Nadr bin Harith’ da ‘Uƙbah ibn Abi Mu’ayt’ ga malamin yahudu (Rabbi) kan bincike gaskiyar annabbatar Manzon Allah ﷺ. 

Rabbi ya ce da su, su tambayi Manzon Allah ﷺ a kan abubuwa 3: 

(i) ASHABUL KAHFI, 
(ii) RUH (RAI), da 
(iii) DHUL-ƘARNAIN

Idan Manzon Allah ﷺ ya ba su amsa daidai, to haƙiƙa shi manzo ne, idan kuma ya gaza bayar da amsa, duk abin da yake faɗa na annabta ba gaskiya ba ne. 

Manzon Allah ﷺ ya ce: “أخبركم غداً عما سألتم عنه”, ma’ana, “gobe zan labarta muku abin da kuka yi tambaya a kai”, bai ambaci “INSHA ALLAHU” ba. Wannan ya sa aka samun jinkirin wahayi, har mushrukan Makkah suka fara tsegumi. Bayan kwana 15, sai Ubangiji ﷻ ya saukar da 'Suratul Kahf' tare da yi mata rakiya da Malaki'u 70,000, banda amsar “ويسـلونك عن الروح ... ” (Isra’i, 17:85).

Ubangiji ﷻ na cewa, cikin aya ta 23 - 24: “ولا تقولن لشيء إني فاعل ذلك غدا إلا أن يشاء الله”, ma’ana: “Kuma kada ka ce da wani abu, ni mai aikatawa ne gobe face (sai ka ce) idan Allah Yaso…” (Ibn Jarir (15/229) & Bukhari 2819) 

2. JARRABAWAR ILIMI  
 
Aya ta 60 – 82: Ibn Abbas رضي الله عنه cikin Bukhari (4725): Wata rana Annabi Musa عليه السلام yana huɗuba, sai wani mutum ya yi tambaya kan, WAYE YA FI KOWA ILIMI? Sai ya ce: “NI NE” bai ce "ALLAH SHI NE MAFI SANI BA"; shi ne Ubangiji ya nuna masa aya da wani mutum, salihin bawa, mazauni bakin kogi (Khidir), ya buɗe masa wasu ilmai (da Allah ya keɓance shi da su).

Ko a kimiyya, Richard Panek (2011) da Aleksey Filippenko (2012) sun ce, idan ka tattare dukkan ilmai game da kaunu (universe/halitta), iya 4% ne mutane suka mallaka, akwai wasu duniyoyi da halittu a sararin samaniyya da har yanzu bincike bai kai ga gano su ba. SANIN KOMAI SAI ALLAH, ALLAH SHI NE MAFI SANI!

3. JARRABAWAR DUKIYA  
 
Aya ta 32 - 45: Labarin wasu mutane ne 2, ɗaya mai gona, mai yalwa, yana yi wa ɗaya gori da cika-baki da taƙama, ganin yana cikin ni’ima da daula, ba tare da tunanin lahira ba. 

Abokinsa ya yi masa nasiha da ya maida komai ga Allah, shi ne ke azurtawa kuma yake sakamako a lahira.

4. JARRABAWAR IMANI

Daga aya ta 9 – 26: Labarin wasu mutane ne 7,  (Y)Amlikha, Maksalmin, Tartus, Nabyunus,  Dabranus, Kafstatyus da Maratonis tare da karensu (Ƙitmir). Sun rayu a zamanin sarki ‘Diƙyanus' (201- 251AD), sarki na 34th a Daular Rum.

Waɗannan samarin sun yi hijira don ƙauracewa bautar gumaki da mulki kama-karya na Diƙyanus. (A WATA RUWAYA) Sun yada zango a wani kogo na yankin ‘Al-Rajib’ na ƙasar Jordan. Jin labarin ficewarsu daga gari, ya sa a ka biyo sawunsu, idan aka tabbatar cewa sun shiga cikin ‘kogo’, sai aka gine ƙofar kogo don yunwa da kishi su kashe su, Ubangiji kuma sai ya sanya musu bacci na tsawon shekara 300 - 309. 

Sun farka sanadiyyar wani mai kiwo ya fasa ƙofar, hasken rana ya haska cikin kogo. Lokacin har an shuɗe wancar daula, an yi sarakuna, da sabbin sauye-sauye da tsare-tsare tsawon shekaru.

Suna farkawa, sai su ka tura ɗaya daga cikinsu (Yamlikha) don ya siyo musu abinci, mutane suka kasa shaida kuɗin hannunsa, suka kai shi ga sarki, aka shaida cewa tun kusan shekaru 300 baya aka daina amfani da irin wannan kuɗin, ya kwashe labarinsu ya ba wa sarki, sarki ya ce su je kogon. Yamlikha yana shiga ya sanar da su, sai suka roƙi Ubangiji ya ɗauki rayuwarsu, don ba sa son dawowa duniyar da ake ta’addanci. 

5. JARRABAWAR KARFI/MULKI  

A aya ta 83-98; labarin Dhur-Ƙain da gwargwarmayar jihadinsa, da kuma kange mutane daga fitinar Yajuju da Majuju. Wannan ya karantar da cewa, duk wanda y aba wa mulki ko dama, zai yi amfani da ita ne domin amfanar da al’umma, ba don fariya, ko tinƙahu da danniyya ba. 

✍️Aliyu M. Ahmad
9th Rabi’ul Thani, 1444AH
4th November, 2022CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #Alkurani #Kahf

Post a Comment

0 Comments