Google Search



Kusan kowa ya san amfanin 𝗚𝗼𝗼𝗴𝗹𝗲 (shi ne 𝗕𝗜𝗡𝗖𝗜𝗞𝗘), amma ba kowa ya san ya ake amfani da shi ba (sosai).

Abin mamaki ne ga wanda yake riƙe da ‘𝘀𝗺𝗮𝗿𝘁𝗽𝗵𝗼𝗻𝗲’ (𝗶𝗣𝗵𝗼𝗻𝗲/𝗔𝗻𝗱𝗿𝗼𝗶𝗱) amma yana wata ƙaramar tambaya (kan yadda zai wani abu (𝗵𝗼𝘄 𝘁𝗼?), ko 𝗻𝗲𝗺𝗮𝗻 𝘁𝗮𝗿𝗶𝗵𝗶, ko 𝗹𝗶𝘁𝘁𝗮𝗳𝗶, ko 𝘄𝗮𝗻𝗶 𝗯𝗮𝘆𝗮𝗻𝗶…) da zai iya samu cikin wayarsa ta hanyar amfani da “𝘀𝗲𝗮𝗿𝗰𝗵 𝗲𝗻𝗴𝗶𝗻𝗲” (mis. Google.com).

Shi 𝗚𝗼𝗼𝗴𝗹𝗲 𝗦𝗲𝗮𝗿𝗰𝗵, ‘𝘀𝗲𝗮𝗿𝗰𝗵 𝗲𝗻𝗴𝗶𝗻𝗲 ne da yake amfani da ‘algorithm’ wajen bawa mai bincike bayanai da suka yi daidai ko kamancecceniya da kalmar binciken mai bincike daga wasu shafukan yanar gizo a cikin ƙasa da 0.38 seconds.

___________________
Abin lura! 𝗚𝗼𝗼𝗴𝗹𝗲 ba shi ke bada amsa ba, a’a, aikinsa kurum ya nemo ma idan za ka sami amsar abin da kake nema ne daga wasu shafukan (*𝘀𝗲𝗮𝗿𝗰𝗵𝗶𝗻𝗴 𝗲𝗻𝗴𝗶𝗻𝗲).
___________________

Bayan 𝗚𝗼𝗼𝗴𝗹𝗲, akwai sauran ‘𝘀𝗲𝗮𝗿𝗰𝗵 𝗲𝗻𝗴𝗶𝗻𝗲 (da yawa) irin su Bing.com, Yandex.com, duckduckgo.com, startpage.com, wiki.com….. da sauransu.

Kusan kowanne abu da muke da tambaya a kai, akwai shi a 𝗶𝗻𝘁𝗲𝗿𝗻𝗲𝘁... 𝗮𝗱𝗱𝗶𝗻𝗶, 𝗸𝗶𝗺𝗶𝘆𝘆𝗮, 𝗳𝗮𝘀𝗮𝗵𝗮, 𝘁𝗮𝗿𝗶𝗵𝗶, 𝗱𝗮𝗯𝗮𝗿𝘂, 𝗯𝗮𝘆𝗮𝗻𝗮𝗶 …

Sai dai Akwai dabarun bincike da ya kamata mu sani.

1. Saboda ƙarancin ‘𝗰𝗼𝗻𝘁𝗲𝗻𝘁𝘀’ cikin 𝗵𝗮𝗿𝘀𝗵𝗲𝗻 𝗛𝗮𝘂𝘀𝗮, sai dai ka yi amfani da 𝗧𝘂𝗿𝗮𝗻𝗰𝗶 ko 𝗟𝗮𝗿𝗮𝗯𝗰𝗶, ko wasu yarukan na 𝗘𝘂𝗿𝗼𝗽𝗲 ko 𝗔𝘀𝗶𝗮.

2. Idan ka yi bincike kan wata kalma a shafin 𝗚𝗼𝗼𝗴𝗹𝗲, a ƙasan ‘𝘀𝗲𝗮𝗿𝗰𝗵 𝗯𝗮𝗿’zai baka wasu ‘𝗯𝗮𝗿𝘀’ guda 8: 𝗔𝗟𝗟, 𝗜𝗠𝗔𝗚𝗘𝗦, 𝗩𝗜𝗗𝗢𝗘𝗦, 𝗡𝗘𝗪𝗦, 𝗠𝗔𝗣𝗦, 𝗕𝗢𝗢𝗞𝗦, 𝗙𝗜𝗡𝗔𝗡𝗖𝗘𝗦 da 𝗦𝗘𝗔𝗥𝗖𝗛 𝗧𝗢𝗢𝗟𝗦.

• 𝗔𝗟𝗟 - ya ƙunshin duk bayanan kan kalmar, ma’anarta, tarihinta… da sauran bayananta.

• 𝗜𝗠𝗔𝗚𝗘𝗦 - zai baka ‘𝗵𝗼𝘁𝘂𝗻𝗮𝗻’ wannan kalmar.

• 𝗩𝗜𝗗𝗢𝗘𝗦 - zai baka ‘𝘃𝗶𝗱𝗼𝗲𝘀’ da za ka iya buɗewa (𝙥𝙡𝙖𝙮𝙞𝙣𝙜) da ake bayani kan kalmar.

• 𝗡𝗘𝗪𝗦 – yana lalubo ma 𝗹𝗮𝗯𝗮𝗿𝗮𝗶 da aka yi kan kalmar daga 𝘀𝗵𝗮𝗳𝘂𝗸𝗮𝗻 𝗷𝗮𝗿𝗶𝗱𝘂.

• 𝗠𝗔𝗣𝗦 – zai baka 𝘁𝗮𝘀𝘄𝗶𝗿𝗮𝗿 idan wannan kalmar take (idan gari ne, mis. ABUJA) ko idan ake 𝘀𝗶𝘆𝗮𝗿𝘄𝗮 (idan kaya ne, mis. NOKIA)

• 𝗕𝗢𝗢𝗞𝗦 – zai baka littafai aka aka yi bayanin kalmar.

• 𝗙𝗜𝗡𝗔𝗡𝗖𝗘𝗦 - kai baka bayanin ƙiddiga ta kuɗi da ta shafi kalmar.

• 𝗦𝗘𝗔𝗥𝗖𝗛 𝗧𝗢𝗢𝗟𝗦 – ana saita yadda za a riƙa gudanar da bincike a 𝗚𝗼𝗼𝗴𝗹𝗲 𝗦𝗲𝗮𝗿𝗰𝗵 𝗕𝗮𝗿. Akwai 𝗩𝗶𝗲𝘄 (yana yin nuna abin da aka bincika), 𝗗𝗼𝗰𝘂𝗺𝗲𝗻𝘁 (littafi, mujalla, ko jarida), akwai 𝗧𝗶𝗺𝗲 (lokacin da aka samar da bayani, misali, karni na 9, ko 1990, ko 2022).

𝗚𝗨𝗗𝗔𝗡𝗔𝗥 𝗗𝗔 𝗕𝗜𝗡𝗖𝗜𝗞𝗘

𝟭. 𝗟𝗮𝗹𝘂𝗯𝗲𝗻 𝗧𝗮𝗿𝗶𝗵𝗶
Idan kana neman tarihin wani mutumi, ko wani gari, ko wata ma’aikata kai tsaye ka sa kalma tare da HISTORY a gabanta.

• TAHIRIN KAFUWAR JIHAR KANO
• GADAWUR HISTORY
• BUBA GALADIMA HISTORY
• HAJJAJ BIN YUSUF HISTORY
• NITDA History
• BUK History
• COCA-COLA

𝟮. 𝗟𝗶𝘀𝘀𝗮𝗳𝗶
Akwai 𝗚𝗼𝗼𝗴𝗹𝗲 𝗖𝗮𝗹𝗰𝘂𝗹𝗮𝘁𝗼𝗿 da zai baka bayanin lissafi da zarar ka sa lissafin 𝐭𝐚𝐫𝐚𝐰𝐚 (+), 𝐝𝐞𝐛𝐞𝐰𝐚 (-), 𝐫𝐢𝐛𝐚𝐛𝐛𝐚𝐲𝐚𝐰𝐚 (𝐱), 𝐫𝐚𝐛𝐚𝐰𝐚 (÷), ko 𝐭𝐫𝐢𝐠𝐨𝐧𝐨𝐦𝐞𝐭𝐫𝐢𝐜, 𝐥𝐨𝐠𝐚𝐫𝐢𝐭𝐡𝐦𝐢𝐜 da 𝐞𝐱𝐩𝐨𝐧𝐞𝐧𝐭𝐢𝐚𝐥 𝐟𝐮𝐧𝐜𝐭𝐢𝐨𝐧𝐬.
Misali, ka sa 𝟱 𝘅 𝟮 a cikin ‘𝘀𝗲𝗮𝗿𝗰𝗵 𝗯𝗮𝗿’, zai baka amsa = 𝟱. Ko 𝟱 𝘅 𝟮(𝟮) = 𝟮𝟬.

𝟯. 𝗦𝗮𝘂ƙ𝗲 𝗟𝗶𝘁𝘁𝗮𝗳𝗮𝗶, 𝗸𝗼 𝗙𝗶𝗹𝗲𝘀
A duk lokacin da kake neman wani littafi, za ka rubuta sunansa, sai ka ƙara harafan 𝗣𝗗𝗙 a gaban sunan misali 𝗥𝗜𝗖𝗛 𝗗𝗔𝗗 𝗣𝗢𝗢𝗥 𝗗𝗔𝗗 𝗣𝗗𝗙, ka kara da FREE (saboda akwai na kudi).

Idan document kake nema, sai ka sa (docs),
• power point = pptx
• excel = xlsx
• subtitle = srt… da sauransu

𝟰. 𝗖𝗮𝗻𝗷𝗶𝗻 𝗞𝘂𝗱𝗶
Za ka iya sanin darajar 𝗡𝗮𝗶𝗿𝗮 zuwa wasu kuɗaɗe misali 𝗗𝗼𝗹𝗹𝗮𝗿 ($), ko 𝗘𝘂𝗿𝗼 (£), ko 𝗥𝗶𝘆𝗮𝗹 ko 𝗬𝘂𝗮𝗻 (¥)…,

Kai tsaye ka sa 𝗥𝗜𝗬𝗔𝗟 𝗧𝗢 𝗡𝗔𝗜𝗥𝗔, ko kuma ₦𝟭𝟬𝟬,𝟬𝟬𝟬 to 𝗗𝗼𝗹𝗹𝗮𝗿 ($), zai baka sakamako.

𝟱. 𝗡𝗶𝘀𝗮𝗻 𝗭𝗮𝗻𝗴𝗼
Idan ka tashi tafiya daga 𝗞𝗮𝗻𝗼 zuwa 𝗔𝗯𝘂𝗷𝗮, za ka iya shiga Google.com, ka sa 𝗞𝗔𝗡𝗢 𝗧𝗢 𝗔𝗕𝗨𝗝𝗔, zai baka adadin 𝗸𝗶𝗹𝗼𝗺𝗲𝘁𝗿𝗲𝘀 (kms) da 𝗮𝘄𝗮𝗻𝗻𝗶𝗻 (𝗵𝗿𝘀) da za ka ci a hanya kafin isa 𝗔𝗯𝘂𝗷𝗮 daga 𝗞𝗮𝗻𝗼.

𝟲. 𝗙𝗮𝘀𝘀𝗮𝗿𝗮
Za ka iya fassara wata kalma ko julma daga yaren 𝗛𝗮𝘂𝘀𝗮 zuwa kowanne yare, ko daga wani yaren zuwa 𝗛𝗮𝘂𝘀𝗮 a ‘Google.com’

Misali, ka sa 𝗛𝗔𝗨𝗦𝗔 𝗧𝗢 𝗖𝗛𝗜𝗡𝗘𝗦𝗘 misali, ko 𝗛𝗔𝗨𝗦𝗔 𝗧𝗢 𝗬𝗢𝗥𝗨𝗕𝗔, ‘𝗱𝗶𝗮𝗹𝗼𝗴𝘂𝗲 𝗯𝗼𝘅’ guda 2 za su fito, daya a hagu na Hausa (𝙮𝙖𝙧𝙚𝙣 𝙙𝙖 𝙯𝙖 𝙖 𝙛𝙖𝙨𝙨𝙖𝙧𝙖) ⇋na dama ARABIC (𝙮𝙖𝙧𝙚𝙣 𝙙𝙖 𝙖𝙠𝙖 𝙮𝙞 𝙛𝙖𝙨𝙨𝙖𝙧𝙖).

𝟳. 𝗡𝗲𝗺𝗮𝗻 𝗙𝗮𝘁𝗮𝘄𝗮
Idan kana neman 𝗳𝗮𝘁𝗮𝘄𝗮 kan wata 𝗺𝗮𝘀’𝗮𝗹𝗮 ta addini, ka ɗauki wata kalma ko jumla cikin mas’alar ka sa a ‘𝘀𝗲𝗮𝗿𝗰𝗵 𝗯𝗮𝗿’ zai baka shafukan da aka (taɓa) amsa tambaya kan irin wannan mas’alar.

Misali, “𝗖𝗿𝘆𝗽𝘁𝗼-𝗰𝘂𝗿𝗿𝗲𝗻𝗰𝘆 𝗶𝗻 𝗜𝘀𝗹𝗮𝗺”, in ka so ka ƙara da ISLAMQA.

___________________
* 𝙉𝙖 𝙛𝙞 𝙮𝙖𝙧𝙙𝙖 𝙙𝙖 𝙠𝙖 𝙩𝙖𝙢𝙗𝙖𝙮𝙞𝙣 𝙢𝙖𝙡𝙖𝙢𝙖𝙣 𝙜𝙖𝙧𝙞𝙣𝙠𝙪, 𝙛𝙖𝙘𝙚-𝙩𝙤-𝙛𝙖𝙘𝙚 𝙠𝙖𝙣 𝙢𝙖𝙨’𝙖𝙡𝙖𝙧 𝙖𝙙𝙙𝙞𝙣𝙞, 𝙨𝙖𝙗𝙤𝙙𝙖 𝙗𝙖𝙢𝙗𝙖𝙣𝙘𝙞𝙣 𝙛𝙖𝙝𝙞𝙢𝙩𝙖 𝙩𝙖 𝙛𝙪𝙨𝙠𝙖𝙧 𝙖𝙠𝙞𝙙𝙖 𝙙𝙖 𝙛𝙞𝙦𝙝𝙪.
___________________

𝟴. 𝗦𝗮𝗻𝗶𝗻 𝗬𝗮𝗻𝗮𝘆𝗶 (𝗪𝗲𝗮𝘁𝗵𝗲𝗿)
Ka sa sunan wurin da kake a ‘𝘀𝗲𝗮𝗿𝗰𝗵 𝗯𝗮𝗿’, sai ka ƙara da Kalmar “𝘄𝗲𝗮𝘁𝗵𝗲𝗿”, misali 𝗛𝗔𝗗𝗘𝗝𝗜𝗔 𝗪𝗘𝗔𝗧𝗛𝗘𝗥.

𝟵. 𝗠𝗮’𝗮𝗻𝗮𝗿 𝗞𝗮𝗹𝗺𝗮𝗿 (𝗮 𝗗𝗶𝗰𝘁𝗶𝗼𝗻𝗮𝗿𝘆)
Google zai tattara duk shafukan da suke bayar da a ma’anonin kalmomi.

Ka yi amfani da waɗannan kalmomi a gaban kalma domin samun bayanin:

• Meaning = ma’ana
• Usage = amfani
• Eytm = tushen kalma
• Quote = zantukan hikima da wannan kalmar

𝟭𝟬. 𝗙𝗮𝗿𝗮𝘀𝗵𝗶 (𝗽𝗿𝗶𝗰𝗲)
Idan kana buƙatar sanin farashin wani kaya a kasuwar yau, misali smartphone, computer, mota… kai tsaye ka sa kalmar sai ka sa PRICE IN NAIRA.

Misali,
• 𝗖𝗢𝗥𝗢𝗟𝗟𝗔 𝟮𝟬𝟮𝟮 𝗣𝗥𝗜𝗖𝗘 𝗜𝗡 𝗡𝗜𝗚𝗘𝗥𝗜𝗔
• TECNO CAMON 19 PRICE IN NAIRA

Za a watso ma bayanin farashin a fuskar wayarka,

𝟭𝟭. 𝗦𝗮𝗻𝗶𝗻 𝘆𝗶𝗻 𝗮𝗯𝘂𝗯𝘂𝘄𝗮 (𝗵𝗼𝘄 𝘁𝗼)
Sau da yawa kana buƙatar yin wani abu a wayarka ko a computer, amma baka san ya zaka yi ba.

Za ka iya tambaya ya ake komai a Google.com, ta hanyar amfani da kalmar “HOW” ko "كيف" da Larabci.

Misali,
• HOW TO OPEN A FACEBOOK PAGE
• HOW TO BACKUP MY FILES
• HOW TO PASS MY EXAM
• HOW TO TREAT MALARIA

𝟭𝟮. 𝗟𝗬𝗥𝗜𝗖𝗦
Za ka iya neman ‘𝗹𝘆𝗿𝗶𝗰𝘀’ (waƙa a rubuce) a Google.com.

Misali,
• HASBUNALLAH JALLALLAH LYRICS
• ADULTHOOD NA SCAM LYRICS
• KADDARAR RAYUWA LYRICS

𝟭𝟯. 𝗦𝘂𝗯-𝘁𝗶𝘁𝗹𝗲 𝗻𝗮 𝗙𝗶𝗹𝗺
Za ka iya neman “sub-title” na wani film, na Indiya, American, Chinese, Turkish, Arabian… a Google.com, ta hanyar amfani da haruffan SRT.

Misali,
• THE MESSENGER ENGLISH SRT
• BAHUBALI English SRT

* BABU ABUN DA ILIMI BAI YI BAYANINSA BA, SAI DAI KA BAKA TAMBAYA BA, KO BAKA LALUMA A GOOGLE BA (mu tuna, akwai karancin 'contents' cikin Hausa, sai dai a yi amfani da Turanci, Larabci, Faransanci ko wasu yarukan Europe da Asia).

Allah Ya amfana.

✍️ 𝗔𝗹𝗶𝘆𝘂 𝗠. 𝗔𝗵𝗺𝗮𝗱
28th Dhul-Hijjah, 1443AH
27th July, 2022CE

#AliyuMAhmad #FasaharZamani #𝗚𝗼𝗼𝗴𝗹𝗲Search #𝗚𝗼𝗼𝗴𝗹𝗲 #SearchingEngine

Post a Comment

0 Comments