Old Boys


Wasu ƙannenmu za su yi old boys, suna son haɗa contribution za su ginawa makarantar da suka kammala aji, suna so na ba su shawara.

Na ce:

Ku fara gina kanku kafin ku gina aji, gina aji ba zai yi muku wahala ba, amma yanzu kun ɗauko abin da ya fi ƙarfinku gaskiya. Maimakon ku yi focusing kan gina taku rayuwar, za ku ƙare a ƙoƙarin gina abin da ya fi ƙarfinku, za ku takura, kuma ba wajibinku ba ne, a ƙarshe ku kuma babu mai gina ku.

Old boys a matakin shekaru 2, 3, 5... da kammala sakandire, ana yi ne don ana ƙarfafa zumunci. Wasu za su je jami'a (su yi karatu), wasu su kafa sana'a; an dai shiga kuma shekarun gwagwarmaya, kowa na ƙoƙarin gina kansa, ya tsaya da ƙafarsa. A wannan matakin, a haɗu a yi zumunci. Idan an yi wani abun murna ga ɗayanku, a haɗu a taya shi murna, haka na jaje.

Kun gana sakandire ko firamare da shekara 1 zuwa 10, ko ma 20; ku focusing kan gina taku rayuwar, kuma kuna zumunci da sauran abokan abokan karatu. Amma yanzu nawa ne kuɗin gina sabon aji? Kuna da shi? Ta ya za ku tara? Za ku je neman taimako ne wajen 'yan siyasa idan ba su ba ku ba ku zage su cewa ba sa taimako? 

Kwananan akwai wata makarantar firamare a Haɗejia da aka bikin cikarta shekara 100 (Abdulkadir Pilot), mutum 1 (Alh. Umaru Abdu mai Crosgrove) cikin waɗanda suka yi wannan makarantar ya ce a yashe duk makarantar (duk) a maida ta ta zamani (renovation), kuma har yanzu ana kan aikin. 

Akwai wasu ma a wata makaranta, sun je taron old boy last year, za su haɗa contribution da kai wa tsofin malamansu ko iyalan waɗanda suka rasu daga cikin malamansu, mutum 1 cikinsu ₦1.5 million ya bayar da contribution nasa shi kaɗai, banda masu ₦500k, wasu ₦100k, kowa daidai da ƙarfinsa.

Idan kana matashi, ka taso da zuciyar son taimakawa al'umma, babban taimakon da za ka fara yi shi ne KA TAIMAKI KANKA, ka tsaya ka gina kanka. Kada ka zagi kowa saboda ka yi wa al'umma hidima, kai kuma al'umma sun ƙi taimakonka (kai ka sa kanka). 

Ba a ce kada ka yi taimako ba sai ka jira ka tara, a'a; idan ka ce sai ka zama hamshaƙi za ka fara taimako ba lalle ne idan ka tara ɗin ma ka iya ba (saboda ba ka sabarwa kanka ba). 

A matakin kun kammala sakadire da shekara 1 - 10, akwai hanyoyi da za ku iya tallafawa 'yan baya daidai da ƙarfinku, kamar tutorials a lokacin jarabawar JAMB, WAEC, NBAIS da NECO, ko kuma haɗa quiz da lectures da za su zaburar da 'yan baya (don dai bada 'yar kyautar littafai, ko jaka ba zai gagare ku ba, bai fi ƙarfinku ba), haɗa career guide, sharing musu experience yadda kuka rayuwa bayan rayuwar sakandire da gwagwarmayar neman admission ko kafa sana'a bayan kammala sakandire, da makamantansu. 

Ka tsaya gina kanka! Kada ka takurawa kanka kan yin abin da ba ka da shi, ya fi ƙarfinka, kuma ba wajibinka ba ne. Za ka iya taimako ne daidai da abin da kake da shi a yanzu.

✍️Aliyu M. Ahmad
14th Dhul Hijja, 1445AH
10th June, 2025CE

#RayuwaDaNazari #AliyuMAhmad #AliMotives

Post a Comment

0 Comments