Kana Confused Age!

Kana tsakiya da confused age (shekarun shakku), kada ka bari wani ya ƙara confusing naka, ko kuma kai ka confusing kanka da kanka.

Mene ne confused age? Shekaru ne tsakanin 18 zuwa 25 na rayuwar matashi, shekarun da kake ƙoƙarin gina kanka ta hanyar neman ilimi, sana'a ko gina wata 'career' tare da karawa da sauran takwarorinsa a duniya. Shekaru ne da matashi ke shiga ruɗani, tsakanin sha'awa, burin duniya, gaggawar samun nasara.... Da ka shiga 26 - 35 kana mid-life crisis; ka fara girbar rayuwar da ka yi a 18 - 25 (ta kuskure, ko daidai).

Kada ka yi tsammanin tara abin duniya a 'yan shekaru 1, ko 2 da fara nema. Kai! Ko kana samu ma, bai kamata ka fara facaka da kuɗi don ka nunawa duniya kana da kuɗi ba. Waɗannan da kake son burge su, sune dai za su yi maka dariya da gori idan ka gaza. Kada kuma a yi tsammanin samun irin abin da wanda ya shekara 10 da fara nema a wajenka kai mai shekara 1 ko 2 da fara nema (idan ba kyauta ko gadon dukiya aka bar maka ba). Ka san kanka, ka san matsayinka, kada ka jefa kanka cikin damuwa.

Idan aiki ka samu, na wani kamfani ko gwamnati, za ka shiga ne as 'entry level' (sabon shiga), kada ka taɓa tsammani samun dama kamar ta director (wanda ya yi shekara 10+ har ya kai matakin da yake). Haka nan, idan kasuwanci ne, ko wata sana'ar hannu; ka bibiyi tarihin waɗanda suka yi nasara, shekara nawa suka yi suna gwagwarmaya ana fafatawa? Wane irin tashi-faɗi da ƙalubale aka fuskanta har aka kai matakin da ake a yanzu? KA BI DUNIYA A SANNU, ka kuma riƙe sababi.

Idan ka samu kuɗi a 18 - 25; 25 - 35; adanawa ake yi domin gobe, ba facaka ake yi don a nunawa 'yan uwa da abokai da 'yan mata, eh; kai ma kana da kuɗi ba. Ai zuba hannun jari (na kadara ko gina kai) ake yi, ko a ajiye wata kadara da darajartar ba ta faɗuwa (don adanin gobe).

Ba fa cewa na yi, kada ka more guminka ba, ka sanya sutura mai kyau, abinci mai daɗi..., a'a; ka dai riƙa lissafin yayin kashe kuɗaɗe. Komai za ka yi, ka riƙa sani, kanka za ka yi wa. Rayuwarka ce, ba rayuwar mutane ba. Da zarar ka 'yantar da tunaninka daga neman yabo da burge mutane, za ka maida hankali ne kan gina rayuwarka, maimakon bayyana ka yi nasara (wacce ba ta gama ɗorewa ba) kana matashi.

✍️ Aliyu M. Ahmad
13th Shawwal, 1446 AH
11th April, 2025 CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments