Domin gujewa shiga ruɗu... (edited).


Domin gujewa shiga ruɗu... (edited).

Saboda muna wani zamani da bayanai sun yawaita (information overload), har hakan kan ruɗar da tunanin matasa, MENE NE DAIDAI? WANE NE A KAN KUSKURE, WANE NE A KAN DAIDAI... duk dai, kafin ka yarda da fatawar mutum ko malami, ra'ayinsa ko wani bayani a ADDINI ko KIMIYYA ko RAYUWA, ka fara duba a wanne fannin ya fi takhassus (specialization). An fi samun ƙofar kuskure daga wanda ba ahalin wanin ilimi ba, idan ya yi kutse cikinsa. Shi ya sa Ibn Hajar Al-Asƙalani a cikin "Fathul Bari" (3/584) ya ce: "من تكلم في غير فنه أتى بالعجائب", ma'ana: "Duk wanda ya yi magana a wani fanni da ba na shi ba, sai ya zo da abubuwan al'ajabi (mamaki)".

Idan likita ne, ya yi magana kan lafiya, misali; likitan wane ɓangare ne? Don mutum yana aiki a ASIBITI ba shi ke nuna ya san komai da komai na jinya ko lafiya ba. Zan fi yarda da bayanin 'ophthalmologist' ko 'optometrist' kan matsalar ido. A matsalar fata zan fi saurarar bayanan 'dermatologist'; sannan na san aikin 'physicians' daban yake da na 'surgeons'. Haka nan, bayanan 'nutritionist' zai fi gamsar da ni kan cimaka...

Idan akan addini ne, ɗalibi ko malamin wanne fanni ne shi wannan mai maganar? Idan a fiƙhu ya ƙware, a wanne fannin fiƙhu? Kasuwanci, ibadar tsarki da salla, zamantakewar aure da rabon gado (Ahwal Shakhsiyya), ko kuwa fikhun hukunci (Jinayat)... Malamin aƙida ne ko hadisi? Ko malamin lugha (harshe) ne kawai? Ko malamin zallar Alƙur'ani Mai girma da ƙira'a ne? Kafin ka yarda da ginawa ko rushe wani hukunci, fara duba matsayin mutum a fannin da ya yi magana. KOWA YANA DA IYAKA! Ba zan wahalar da kaina ko jin mamakin bayanin Salafi/Athari, ko Ash'ari, Maturidi, ko Bamu'tazile ko Jahami kan Tauhidi ba, ba na tsammata komai fiye da abin da aƙidar da mutum yake kai. 

Eh! Kana da ilimi addini, ko ka iya larabci, amma ba kowanne fanni ne ka san komai da komai ba. Ko PhD ne da kai a ilimin Ƙira'a, ba laifi ba ne don ka jahilci wani abu a fiƙhu ko hadis, ai "الإنسان مهما بلغ من العلم، يظل جاهلاً بأمور كثيرة", ma'ana: "Mutum duk cikar a ilimi, har yanzu yana jahiltar abubuwa da dama (koda kuwa a fannin nasa ne ma).

Ko a ɓangaren tattali, siyasa, zamantakewa... sai na lura da mazhabar mutum. Ba lalle ne sai mai ilimi ya san komai da komai, kowa yana iyakar ilimi. Misali, ka ɗauki fuskar bayani ko fatawowin kan tattalin arziƙi, Sunusi Lamiɗo Sunusi Monetarist/Institutional Economist ne, Patrick Utomi kuwa Neoliberal ne, Banji Oyelaran kuwa Structuralist ne, kowannensu yana bayanin tattali ne ta fuskar da ya gina iliminsa, gogewa da aƙidarsa kan tsimi-da-tanadi (Economics).

Duk da haka, WANNAN BA ZAI HANA KA KARƁAR GASKIYA IDAN TA BAYYANA DAGA WANI BA, KO DA BA FANNINSA BA NE, kamar yadda ta faru da Ibn Sakhr Addawsi da Sheɗan kan Ayatul-Kursiyyi ba (Bukhari, 2311). Amma kafin ka nutsa, ka saurari me 'yan wannan gidan (fannin) suke bayani. Idan ya yi daidai da bayaninsa, fani'im, idan ya saɓa, ka sake bincike. Ko a gidan Shari'a (Law) na experiencing fatawowi daga malamai suna saɓawa, mai Public Law, ya kan iya zamewa kan Civil ko Corporate Law. Hakan nan a gidan Linguistics, tsakanin 'Structuralists/Formalists', masu Morphology da Syntax, da masu duba ma'ana Semanticians da Pragmaticians ko masu Discourse. Yawanci an fi samun ruɗu daga lokacin da baƙin ahalin wani ilimi suka yi masa kutse, musamman na addini, العلم بحر لا ساحل له، وما نعلمه قطرة مما نجهله. Duk yadda ka kai ga ƙaunar malami, mai ilimi ne a fannin da ya kware, zai iya samun ƙarancin sani a wasu fannika da ba na shi ba.

Sanin wannan zai taimaka sosai don kada ka ruɗu da jin sabbin abubuwa na ilimi. Shi ya sa a majalissan tarbiyya, tun kafin ka karanta littafi sai ka nazarci tarihin mawallafi, lokacin da aka haife shi, iyayensa da muhallinsa, malamansa da gwagwarmayarsa a rayuwa da neman ilimi. Sanin wannan zai rage maka shiga ruɗu a matsayinka na matashi daga ɗebo kowanne irin yayi kana sakawa a kanka, ko maka riƙa shiga ruɗu rashin gane daidai da akasin haka.

A dai kuma daure a yi karatu!

✍️Aliyu M. Ahmad
6th Ramadan, 1445 AH
16th March, 2024 CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments