Kai ɗan uwana matashi, wayayye


Kai ɗan uwana matashi, wayayye:

Duk abin da ka gani a Musulunci, kake da KOKWANTO a kai, ka nemi MALAMAI, masana fannin mas'alar, don su yi maka bayani don ka wanke kokwantonka da zato-zatonka.

Matuƙar ba ka yi karatu ba, ba ka da ƙarfin tunanin da za ka fassara mustalahaat da masa'il na abin da ba ka karanta ba, ba ka da ilimi a kai, sai dai zato kawai.

Kamar ma fa Musulunci muka raina ko?
Mun raina addini ne gaskiya.

A jami'a, kowannen fanni ma kake karanta, daga Arts, Humanities, Social Sciences, Sciences, Techs... yana daga cikin scheme, idan aka tambaye ka ka yi 'defining' wani 'term', sai ka backing bayaninka da fassarar da masana wannan fannin suka yi, kafin ka ƙara da abin da kai ma ka fahimta. Ba ka isa ka defining wani terms a kai ɗalibi, to kai waye a fagen da za ka iya zama hujja?

Haka nan, idan ka tashi 'research', ba ma za ka fara koro bayani ba, sai ka fitar da abin da waɗanda suka gabace ka a ilimi kan (Literature Review), mene ne haƙiƙanin ma'anar mustalahaat (terminologies) da suka shafin research da kake yi don ka fitar da daidaito kan abin da kake son yin magana a kai.

Ba ma wannan ba! 

Idan jinya kake a yau, kai da ba ka da ilimin likitanci, in dai ba ganganci za ka yi ba, karan-tsaye; sai dai ka je asibiti wajen masana jinyarka, consultants: cardiologist, ko neurologist, oncologist, dermatologists, ko dentists, ko ophthalmologists, ko pulmonologist, ko likitan ɓangaren mata gynecologist ko obstetricians... Kai wani likitan ma idan jinyarka ba ɓangarensa ba ce, zai referring ɗinka zuwa wajen wanda specialty nasa ce.

Me ya sa ba ka zauna ka treating kanka da kanka a gida ba, ka je asibiti? Sai jinyar (jahilci) da ka yi wa addini ce kake ganin ka isa zamar wa kanka likita (mufti)?

Me ya sa idan wayar hannunka (smartphone) ko babur (motorbike), ko motarka, kai ko ginin gidanka ko wutar lantarki... idan suka sami matsala, kai kuma ba ka da kwarewa a kai, sai dai ka je ka ɗauko wani MASANI KWARARRE ya gyara maka? Haka ma addini yake, akwai waɗanda suka shafe shekaru suna karatu da warware matsalolin (jahilci) da suka shafi fannoninsu.

Idan ba addini ka raina ba, me ya sa kake yi wa addini karan-tsaye? Su kuma waɗancan misalan na sama (jinya, lalacewa) kake yin takatsantsan, tare da maida su ga masana don kada ka sami matsala? Yi wa addini karan-tsaye ba abin da zai jawo maka face halaka, idan ma ba ka halaka a duniya ba, za ka haɗu da Ubangiji ﷻ a ƙiyama.

Yadda dukkan fannonin ilimi suke da mustalahaat (terminologies) da nazariyyaat (theories), haka ma a Musulinci dukkan fannoninsa suna da na su usul da ƙawa'id.

CAPITAL WARNING ⚠️ Ubangiji ﷻ ya yi mana a cikin Alƙur'ani, Al-Isra' aya ta 36 "ولا تقف ما ليس لك به علم", ma'ana "Ka da ku bi abin da ba ku da ilmi a kai", cikin An-Nahl aya ta 116 kuwa aka ce, "Kada ka ce wannan halas ne ko haram don ka kirdadowa Ubangiji ƙarya..." cikin Hajj aya ta 3, saboda Ubangiji yana sane da kowa, ya ce: "A cikin mu, mu mutane, akwai waɗanda suke jayayya da Ubangiji ba tare da ilimi ba...". Mafita, cikin Al-Anbiya aya ta 7, KU TAMBAYI MASANA IDAN KUN SAN BA KU SANI BA".

Neman ilimin addini kuma wajibi ne, ba sai ka tara ka zama babban malami kamar Sheikh wane ko malam wane, amma dole ne ka yi addini da ilimi, tare da kiyaye kai daga shiga abin da ba ka da ilimi, ko yin musu da jayayya. Ka ji wata ƙadiyya tana TRENDING a social media, ka tambayi kanka, kana da ilimi a kai? Ka taɓa karanta wani abu a kanta a baya? Stay away daga abin da ba ka da ilimi, kada ka jefa kanka a halaka. Ka koma gefe ka zama ɗalibi, za ka kwashi ilimi.

✍️Aliyu M. Ahmad
9th Ramadan, 1446 AH
9th March, 2025 CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments