Ohhhh dama haka ne?
To bari ka ji!
Wani lokacin, rashin karatu ko rashin fahimta ke sa mutum ya ji kamar ba shi da wata nasara a rayuwa. Kada baƙin kalmomi su ruɗe ka, na Turanci, Larabci, ko wani harshe har ka ji kamar ba ka da wata daraja ko abubuwan zamani. Abin da kake buƙata shi ne ILIMI, domin ya sa ka gane haƙiƙanin MATSAYINKA da HANYOYIN INGANTA KANKA.
Misali:
1. Manufa (Goal)
Kullum za ka ji ana maganar manufa a rayuwa, "matasan yau ba su da manufa!" Amma idan kana da sana’a, aiki, ko kai ɗalibi ne, to ai kana da wata manufa da kake gina gobenka da ita. Misali: Idan kana karatun professional course (LLB, MBBS, da sauransu), ka san me kake shirin zama bayan ka gama, lauya ne, ko likita, ko injiniya (karatun da shi kake gina manufar gina 'career'). Idan kana kasuwanci, ka san inda kake ƙoƙarin kai kasuwarka. MARAS MANUFA shi ne wanda ba ya yin komai, ba ya da shiri ko tsari na rayuwa.
2. Kwarewa (Skills)
Kada ka ji cewa, wai sai kana aiki da kwamfuta (computer) ne kawai za a ce kana da SKILLS. Skill kalmar Turanci ce kawai, da a Hausa ke nufin 'KWAREWA'. Tela, kafinta, direba, ɗan kasuwa, birkila (magini), ko mai su (kamin kifi), duk suna da skills na ɗinki, kafintanci, kasuwanci, gini, tuƙi... Skills yana nufin kwarewa a kowace sana'a, ba lallai ta kasance a ofis ko a gaban screen na computer ba, don't ever feel small for yourself! Abin da ya kamata ka yi shi ne ka nemi hanyoyin tafiya da zamani don ka bunƙasa ka kanka.
3. Aiki (Career)
A aikace, ayyuka suna kasu kashi uku:
• Samarwa (Production) – Misali: noma, kiwo, kamun kifi, haƙar ma’adinai (mining).
• Sarrafawa (Processing) – Misali: kamfanoni, matatun mai (refinery), da masana’antu.
• Tafikarwa (Services/Distribution) – Misali: aiki a ofis, kasuwanci, kiwon lafiya, sufuri (transportation), tallace-tallace, koyarwa da sauransu.
A kowanne mataki kake, yana da daraja, kuma 'career' ce. Komai ƙanƙantar abin da kake yi, yana da muhimmanci, kai yi ƙoƙari zamanantar da kanka, GOBENKA TA FI YAU. Misali, rumfa ce kake da ita ta siyar da shayi ☕? Sai ka gyara ta ta zama Tea Spot. Kayan gwari (fruits) kake siyarwa? Gyara wajenka, ka mayar da shi Mixed Fruits da Fruit Salad na zamani. Awara kike siyarwa? Ki gyara ta ta zama special awara mai armashi da sabon tsari. Kowacce 'career' da kake gani, akwai Kamayenta (na ƙasa), akwai kuma Ɗangotenta (na ƙololuwa).
4. Ilimi/Tarbiyya (Education)
Idan ka yi karatun boko, madalla. Idan ka yi karatun tsangaya ko zaure, shi ma ilimi ne. Abu mai muhimmanci shi ne ka san yadda ake tafiyar da rayuwa a zamanance, koda ba ka sanu ikon yin boko ko boko mai zurfi (digiri) ba.
Duk mutumin da Ubangiji ya halitta, yana buƙatar abinci, sutura, da muhalli. Waɗannan abubuwa ba za su samu ba sai da kuɗi. Kuɗi kuma sai da aiki da za ka bayar da ƙima (value) a maye gurbin value naka da kuɗi. Mu nema namu ne, arziƙi na Allah ne. Allah yana taimakon wanda ke ƙoƙarin taimaka wa kansa, ko da kafiri ne. Ka tashi tsaye don rayuwarka, ka gina gobe tun yau!
✍️ Aliyu M. Ahmad
13th Sha'aban, 1446 AH
11th February, 2025 CE
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives
0 Comments