Ka Zama Mai Tawali'u!


Be humble!
Ka zama mai ƙanƙan da kai (tawali'u).

Ba a gorantawa ɗan Adam ni'imar duniya, ga mai hankali, komai yin Ubangiji ne. Idan kana tunanin samun ɗaukaka ne ya sanya ka yi wa ɗan uwanka mutum ɗagawa da gani-gani, والله يرزق من يشاء بغير حساب, Ubangiji ﷻ kan azurta bayinsa ba tare da ya yi shawara da KAI ba.

Kada ka yi wa maras kirki mu'amala ta rashin kirki, ka yi wa kowa mu'amala da irin naka halin na kirki. Idan kana da halin kirki da nagarta, kada halin wasu marasa kirki ya hana ka nuna nagartarka gare su.

Ka girmama dukkan 'yan Adam a matsayin mutane, Allah ya yi mutum da daraja "ولقد كرمنا بني آدم", Ubangijinka ya ce ya karrama shi, kai kuma kai ka sanya masa sikilin, sai mai dukiya, mulki ko wanda za ka mora kaɗai ne ke da daraja a idonka? Ba ka san abin da Ubangiji ya ɓoye a cikin bayinsa ba, ba ka abin da gobe ta riƙa ba na sauƙewa da ɗora bayi bisa nasara ko ƙasƙanci, ba ka ma san waye zai taimake ka ba a gobe.

Daga ka sa dukiya, mulki ko mamora a matsayin ganin ƙimar mutane; a yau, wani zai wani gari ba kowa ba, a gobe Ubangiji ya ɗaga likafarsa. A yau wani zai wani gari a matsayin wani, sai Ubangiji ya jarrabe shi da ƙasƙanci, asara, jinya abar ƙyama. A yau kana da ƙarfi, gobe ƙaddara ka iya sauya maka.

Always be humble!

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments