Sunana Aliyu M. Ahmad
Ni ɗalibin nazarin alaƙar yanar gizo (social media in particular) da yadda mutane da mu'amala da ita (NETNOGRAPHY), ina kuma da horo kan bin diddigi (FACT-CHECKING).
Ina da saƙon da nake son na ba wa iyayena MALAMAI, da yayyena ƊALIBAN ILIMI game da social media, wanda na san saƙon zai isa gare su.
Don Allah!
Idan kun zo mumbarin huɗubar Juma'a, ko wurin da dubban mutane ke sauraronku.
Ko kuma, idan kun zo majalissin karatu, wurin da dubban ko ɗaruruwan al'umma ke sauraronku, a zahiri da kuma social media.
Don Allah ku daina ambaton sunayen waɗanda suka yi kaurin suna wajen yaɗa baɗala a social media. Ku dai ambaci ɓarna, da illolinta ba tare da buga misali da wanda BA ZA A ƊAUKI IZINA A KANSA BA. Har wani maɓarnaci ya kai darajar a ambaci sunansa a cikin masallaci?
Kun san dalili?
A lokacin da kuke ambato masu ɓarna, a lokacin wani da bai san su ba zai garzaya shafinsu, don ya ganewa idonsa irin labarin da kuke ambatawa a majalasin karatunku.
Wani ma a lokacin da kake huɗubar Juma'a, saboda kada ya manta, ana cikin huɗuba zai yi 'searching' sunan wannan da aka ambace shi, ko ya rubuta don kada ya manta (na ga wannan misalin).
Ba kwa mamaki ganin maimakon wanda yake baɗala a guje masa, amma sai ya ƙara samun influence, mabiyansa su ƙara ƙaruwa? Yawan ambatonsu yana daga cikin abubuwan da suke ƙara musu sanuwa, da kuma ƙarin engagements.
Za iya nasiha da faɗakarwa ba tare da an ambaci, ko ba wa mutane adireshin wurin da ake aikata ba. Za a iya tare yaɗuwar ɓarna ta rashin ambaton wuraren da ake aikatawa.
Wani zai ce ambaton mai laifi, ba laifi ba ne. Me ya sa Alƙur'ani yake ambaton masu laifi?
Yana daga cikin hikimar Alkur'ani da yake kawo labaran wasu maɓarnata a baya, har aka ambace su a cikin Alƙur'ani, irinsu Fir'auna, Samaduwa, mutanen Lut, da sauransu... amma su tare da izina a labarinsu. Su kuma na yanzu, suna raye, sai ma ƙara samun ɗaukaka da kuɗin shiga (monetization) suke ta hanyar samun enagegements. Wannan ya sa wasunsu ke cewa, hassada ake yi musu, kan abubuwan da suke yi suna samun kuɗi (kada su waɗannan ban san izinar da za a ɗauka a aiyukansu ba a yanzu).
A media, akwai dabaru da dama (BAIT), da su masu barna kan yin amfani da su don jan hankali mutane, daga ciki akwai CLOUT CHASING da ENGAGEMENT FARMING, za su yi abin da za a riƙa ambatonsu ne don su ƙara samun engagement, su tafi VIRAL, mu kuma muna ƙara ba su FREE PROMOTION ta hanyar ambatonsu, mutane su ƙara bibiyarsu. Babu wani maɓarnaci da yake samun raguwar followers, sai ma ƙaru, why?
Za a iya sanya ayoyi da hadisi, da maganganun hikima da suke da alaƙa da laifi don ba wa al'umma tarbiyya. Mun sani, kowacce rai sai wanda Allah ya tsare, zai iya tafiya ga wurin da aka ba shi adireshin baɗala don ya ganewa idonsa. Ubangiji ﷻ ya yi mana umarni mu yi amfani da hikima wajen wa'azi, a wasu wuraren kuma ya yi mana gargaɗi kan taimakekkeniya kan (yaɗa) aiyukan ɓarna.
Ba ma daidai ba ne ka yi tunanin wai an ba wa wani kwangilar su zo rusa tarbiyyar mutane, a'a; 'yan iska akwai su a jiya, akwai kuma na yau. Na yau da muke gani, sabbin sanfuri ne na 'yan iskan zamani da social media ta ba su damar bayyana kansu.
Allah ya sa mu fahimta,
Allah ya sa mu faɗa ka.
✍️Aliyu M. Ahmad
11th Sha'aban, 1446 AH
9th February, 2025 CE
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives
0 Comments