Tsakure IV: Gina Manufa

#Tsakure (Excerpts):

Yawancin mutanen da suka yi NASARA a rayuwa, suna da TARIHI IRI ƊAYA, sun fuskanci shakku da ƙalubale iri ɗaya a farkon tashinsu daga mutanen da suke kewaye da su ('yan uwa da abokai), sune suke fara kashe musu gwuiwa, da saka musu shakku, da ƙasƙanci.

Sune suke nuna musu ba su isa ba, 
Ba za su iya ba, su cika su da shakku.

Da kalamai na nuna musu ƙasƙanci, da kashe gwuiwa, maimako ƙarfafa su, ko ma su taimake su idan suna da hali.

Wadanda suka biye wa maganar mutune, sai su sare, su gaza, su watsar da tafiyarsu, sai su ci gaba da tafiya kamar yadda mutane suke so, ba su assala komai ba.

Waɗanda kuma suka san cewa manufarsu mai iyuwa ce (achieveble), kuma suka fuskanci abin dake gabansu, za su ci gaba da cimma muradansu, har su yi nasara.

Wannan tarihin ba a ƙasar Hausa ba ne, ko a Nijeriya kaɗai, tarihi ne mai tsayi, na waɗanda suka yi nasara a tarihin duniya, misali:

Manzon Allah ﷺ babban misali a farkon fara da'awar Musulunci. Waɗanda suka fara son durƙusar da da'awarsa, 'yan uwansa ne, makusanta. Duba kuma tarihin Annabin Allah Yusufa عليه السلام.

Duba Albert Einstein, Jack Ma, Thomas Edison, Mark Zuckerberg, Bill Gates... Wani da yake nesa zai ga BAIWARKA, har ya iya tallafa maka, amma wani kuma MAKUSANCI (aboki ko ɗan uwa) sai ya gan ka kamar abokin takara (competitor), yana tsoron za ka ɗara shi, shi ya sa yake nuna halin ƙaguwa (crab 🦀), don ya hana ka tashi.

Abu ne mai kyau, bayan ka shirya manufarka, ka kuma yi imani ka tanadi guzurin cimma manufarka, to yarda wani, ko yabo ko kushe ba za su dame ka ba. Shi ya sa, yana da kyau ka sirrinta tafiyarka, RAYUWARKA CE BA TA WANINKA. Annabin Allah Yaƙub عليه السلام, ya gargaɗi Annabi Yusuf عليه السلام kan sirrinta baiwarsa ga 'yan uwansa makusanta, saboda tsoron kaidin 'yan uwansa, zai ɗara su a falala. Amma kuma Aziz da babu dangi iya, babu na baba, ya ga wannan baiwar har ya yi masa naɗi muƙami mai girma.

Akwai darussa, labarai masu darussan, ta fuskar addini, rayuwa, da kuma kimiyyar zamantakewa da halayyar ɗan Adam a cikin GINA MANUFA.

✍️Aliyu M. Ahmad
25th Rajab, 1446AH
25th January, 2025CE

#AliyuWrites #GinaManufa
#AliyuDaManufa #ManufaExcertps
#Tsakure #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments