Soyayya

 ❤️SOYAYYA ❤️


Soyayya wata halitta ce da Allah ke sanya ta cikin zukatan bayinsa ba tare da yayi shawara da su ba, da nufin su zamto ma'aurata domin samun nutsuwa ga kawunansu (Ar-Ruum, aya ta 22) ko kuma a jarabce su da ita domin gwada imaninsu (Al-Baqara, aya ta 155)


Akwai manufofi da dama da suka ɗamfaru da soyayya, amma babbar manufar shi ne "AURE'. 


A matsayinka na matashi kuma Musulmi, mai ilimi da cikakken hankali, ba zaka aikata wani aiki ba, face ka nemi mene ne matsayar Shari’a a kai (ولا يحل له أن يفل فعلا حتي يعلم حكم الله فيه... [Akhadary, p. 3]).


Kusan abu ne a bayyane, da zarar matashi ya dan tasa, zuciyarsa zata fara ƙaiƙayi, soyayyar (wata) zata fara fizgar zuciyar ka. Ibn Qayyim رحمه الله cikin الداء والدواء a shafi na 552 yake cewa:


" وأما محبّة النِّسْوان فلا لوم على المحِبّ فيها ، بل هي من كماله " .


“Babu laifi don wani ya ji yana son wata mace/mata, ba komai/laifi akan wanda yake soyayyar, face ma alamu ne na cikar namiji”.


• MATSAYIN SOYAYYA A SHARI'AR MUSLUNCI;


Soyayya halal ce, idan aka yi ta ta halastacciyar hanya, sannan kuma haram ce, idan aka yi ta ta wata fuskar da addini ko al'ada basu aminta da su ba [روضة المحبين p. 147].


Soyayya daya ce daga cikin ni'imomi da Allah Ya halitta tsakanin jinsi guda biyu (mace da namiji) domin samun nutsuwa da jinkai [Ar-Rum, aya ta 21]. Ta wani bangaren kuma, jarrabawa ce, cikin manyan jarrabawowi da Ubangiji ke jarrabar bayinsa [Al-Baqara, aya ta 155].


So tamkar kayan maye yake, domin wanda ya sha kayan maye ba shi da karfin ikon sarrafa kansa. So cuta ne, cuta da take kama zukata da tunani (مرض نفسانى), cuta ce dake sanya wasiwasi, rashin nutsuwa (wani lokacin) tare da bautar da zukata [روضة المحبين, shafi na 255].

 

• MANUFAR SOYAYYA


A shari’ah, ana gina soyayya tsakanin namiji da mace ne da manufar zama tare har abada (aure) ‘لم نرَ للمتحابَّيْن مثل النكاح’ [Ibn Majah, 1847]. 


Duk soyayyar da bata da manufa, batawa juna lokaci ce.


• WA YA KAMATA NA SO?


Akwai abubuwa da dama da suke jan hankali ka ji kana son mutum. Shi ya sa Annabi ﷺ ya ce:


 تنكح المرأة لأربع لمالها ولحسبها وجمالها ولدينها فاظفر بذات الدين تربت يداك


"Ana auren mace domin abubuwa hudu: domin dukiyarta, ko dangantakarta, ko kyawunta, ko addininta, amma ka rinjayar da mafificiyar addini, hannun damarka sai ya yi turbaya (domin daga karshe zaka kasance mai nasara).” [Bukhari, 4802].


• TA YA ZAN FARA NEMAN SOYAYYA?


1. Ka nemi zabin Allah (ka yi Istkhara), domin neman dacewa da abokiyar/abokin zama na gari, ka kuma yi shawara da mutanen kirki kan kudirinka [Bukhari, 1166]. 


Yana da kyau idan ka ga wata kana son ta , tun kafin ka tunkare ta; ka fara neman zaɓin Allah a kan al'amarin, inshaa Allah idan alkhairi ne za a dace. Kar ka dubi kyau, ko dukiya, wajen neman soyayya; ka dubi hali, da addini. Domin da hali ake zama a gidan aure.  


2. A ka’idar Shari’a, ba zaka fara yiwa ‘mace’ magana ba, ba zaka nemi soyayyarta ba, har sai ka nemi amincewar iyayenta/waliyanta domin baka izinin neman soyayyarta [فقه الحب, p. 19].


3. Kuskure ne babba, kuma zalunci ne ka mallake zuciyar mace ba tare da izinin mahaifanta ko waliyanta ba, ko kuma babu niyya ko halin yin aure a tare da kai. 


Allah (SWT) Yake cewa:


وليستعفف الذين لا يجدون نكاحا حتى يغنيهم الله من فضله


Ma’ana: “Kuma wadan nan da ba su sami aure ba, su kame kansu, har sai Allah Ya wadatar da su daga falalarSa.” [Nur, aya ta 33].


A wani hadisin kuma, Manzon Allah ﷺ Yana cewa:


 يا معشر الشباب من استطاع منكم الباءة فليتزوج فإنه أغض للبصر وأحصن للفرج ومن لم يستطع فعليه بالصوم فإنه له وجاء.


“Ya ku taron samari! Wanda ya samu ikon aure daga cikinku to lallai ne ya yi aure, domin lallai shi ya fi tsarewa daga gani (ido) kuma ya fi tsarewa daga farji. Wanda ba shi da ikon yi, to,’ lallai ya rika azumi don haka shi ne kariyarsa daga zina.‛ [Bukhari, 5066].


4. Idan ka nemi soyayya ba a amince ma ba, ka yi haƙuri, ka dauki hakan a matsayin ƙaddara. Kada ka yi kuskuren soyayya ko auren wacce bata ƙaunarka. 


Shaykh al-Islam Ibn Taymiyah رحمه الله yake cewa: 


فأما إذا ابتُلى بالعشق وعف وصبر فإنه يثاب على تقواه لله


“Duk wanda aka jarraba da soyayya, in har ya kiyaye mutuncinsa, ya yi hakuri, Allah zai ba shi ladan wannan...” [مجموع الفتاوى، 10/133].


Misalin irin haka ya faru a zamanin Manzon Allah (SAW), a wani hadisin Imam Bukhari (hadisi na 5283), Ibn Abbas ya hakaito labarin Mugheeth mijin Barira (wata ‘yantacciyar baiwar Nana A’isha), cewa, ta kai ga an daura musu aure, amma Barirah ta guji Mugheeth saboda bata son sa. 


Mugheeth har kuka yake a cikin mutane saboda soyayyarta. Har wata rana Manzon Allah ﷺ Ya kira ta, yake ce mata “Me yasa ba zaki koma gare shi ba?” Sai ta ce: “Ya Ma’aikin Allah, umarni ne kake ba ni, na koma gare shi?”, Sai ﷺ Ya ce: “A’a, ina son na sasantaku ne kurum.” Sai ta ce: “Tom gaskiya bana son sa.” Sai ﷺ Ya bar ta ta tafi. An ce Mugheeth har ya kare rayuwarsa yana kuka akan soyayyarsa ga Barirah. 


• ABUBUWAN LURA A SOYAYYA


1. Ka gina soyayya bisa gaskiya, ba a gina soyayya a kan ƙarya. Duk soyayyar da aka gina ta kan ƙarya, a karshe za ta rushe ne. Bal karya haramun ce, kuma tana daga cikin manyan laifuka [Yunus, aya ta 69].


Masu hikima na cewa "soyayyar da aka gina ta da tubalin gaskiya, ba zata taɓa rushewa ba. 


2. Shari’a bata yarda ka kebe da matar da ba muharramarka ba (daga kai, sai ita) ba tare da wani makusanci (ko da yaro ne mai wayo) a tare da ku ba [Bukhari, 5233].


3. Haramun ne, nema a kan nema, domin hakan na jawo gasa, fitina, munafurci, wasiwasi da rashin kwanciyar hankali tsakanin masoya [Bukhari, 5142].


4. Marowaci baya soyayya, soyayya sai da kyauta da kyautatawa [فقه الحب, p. 58].


5. A kula da sanya suturar da Sharia ta amince mace ta sanya. Bal! Iya fuska, tafin hannu da kafa ne kurum aka amince namiji ya kalla a jikin matar da ba a daura musu aure ba. Duk inda ya kalla bayan wadannan gabban ka yi haramun [Bidayatul Mujtahid 3/10].


Ya Allah! Ka hada mu da masoya nagari, masu kaunar mu don Kai.


✍️ Aliyu M. Ahmad

22nd Shawwal, 1443AH

23rd May, 2022CE

Post a Comment

0 Comments