IDAN KANA DA IYAYE MASU YAWAN TAKURAWA KO NUNA HALIN KO'IN-KULA



Idan mutum ya nemi shawarata game da jarrabawar iyaye, saboda yawan takurawa, ko nuna halin ko'in-kula; sai dai na ce masa, ya yi hakuri ya karba a haka.


Iyaye dai ba a canja su, kimarsu tafi karfin a bijere musu, komai suka baka umarni matukar ba sabon Allah ba ne, ka daure ka yi musu biyayya, albarkar wannan biyayyar sai Allah Ya daga darajarka, Ya baka kariya daga wani sharrin duniya da lahira.


Idan kuwa ka bijere musu, matukar ba akan sabon Allah suka umarce ka ba, duk yawan ibadarka, sai Allah Ya jarrabe ka, komai taka-tsantsan dinka.


A cikin hadisin Jurayj رحمه الله, Imam al-Bukhari ya kawo shi a cikin Sahih nasa, hadisi na 3436, Imam Muslim hadisi na 2550 cewa; Jurayj ya kasance bawan Allah mai ibada, an ce saboda yawan ibadarsa, kaura ya yi daga cikin gari ya koma bayan gari don ya samu nutsuwar bautawa Allah. 


Wata rana ya sallar nafila, sai mahaifiyarsa ta zo, ka kira sunansa tana cewa: "Jurayj, ni ce mahaifiyarka, ka amsa min." Alhalin shi kuma yana sallah.


Shi kuma a zuciyarsa yana cewa: "Ya Ubangiji! Mahaifiyata ko Sallah?" Sai ya zabi ya ci gaba da Sallar. Ta sake kiransa a karo na biyu, bai amsa ba; sai ta tafi ta mai fushi da shi, sai ta daga hannu ta yi masa mummunar addu'a cikin bacin rai. 


Kafin ya mutu/rasu sai aka jarrabe shi da wata mata (karuwa), har ta kai su ga shariah kan kazafin ya yi mata ciki. * Mu tuna, Jurayj bawa ne salihi, mai bauta da gaske.


Ta wata fuskar kuma, za mu iya dauka izna daga abin da ake hakaitowa daga tarihin Ramesses II (Fir'auna na zamanin Annabi Musa عليه السلام) sanadiyyar biyayya da dawainiyya da yake da mahaifiyyarsa.


1. Gidansu ba jinin sarautar Misra (Egypt) ba ne, saboda bayan mulkin Fir'auna Akhenaten, mahaifinsa ya karbi mulki, yana dan shekara biyar, daf da rasuwar mahaifinsu (Seti), babban yayansu shi ma ya rasu, shi ne aka bashi 'yarima mai jiran gado' daga baya ya zama Fir'auna na II a Daula ta 19.


2. Fir'auna Ramesses II, sanadiyyar biyayyar da yake yiwa mahaifiyyarsa, tun ma kafin zuwan Annabi Musa عليه السلام an sha yin kokarin kifar da mulkinsa, amma an gaza. Har yaki aka gwabza na Kadesh 1274BC (kafin haihuwar Annabi Isah عليه السلام) da sarkin daular Hitti, Muwatalli na II ya kimtsa, amma ba a yi nasara a kansa ba. Sai ma kwace wasu yankuna na Hitti da ya yi.


3. Fir'auna Ramesses II, sanadiyyar biyayyar da yake yiwa mahaifiyyarsa, Allah Ya daukaka shi, ya ba shi karfi a zamaninsa, ya gagari duk dauloli da suke kewaye da shi. A karshe ma ganin ya yi karfi, ya kira kansa cewa, shi ma Ubangiji ne, a cikin Ubangijin ma, shi ne babba [Nazi'at, aya ta 27] wa'iyyazu billah.


4. Allah Ya tsawaita masa rayuwa, ya ba shi karfi da mulki, sai da ya yi shekaru 66 (1279 zuwa 1213 BC) yana mulki a Misra duk da ta'asa da fasadi da yake a bayan kasa, duk dai sanadiyya biyayyawa ga mahaifiyyarsa.


5. Ubangiji ya jinkirta masa azaba, saboda dawainiyya da yake da mahifiyyarsa, sai bayan da ta rasu, duk da Annabi Musa ya roki Ubangiji ya halarka da shi, da mutanensa [Yusuf, aya ta 88]. 


Yiwa iyaye biyayya tare da hakuri da dabi'unsu ko ya suke, shi kurum abin da 'ya'ya za su yi, su sami nasarar rayuwa, duniya da lahira. 


Allah Ya ba mu ikon kyautata musu, amin. 


✍️ Aliyu M. Ahmad

20th Shawwal, 1443AH

21st May, 2022CE

Post a Comment

0 Comments