ME KAKE YI A YAU DON CIMMA MANUFARKA TA GOBE?


Idan kana son gane kyawun gobenka (ma'ana, gobenka za ta yi kyau), ka duba aiyukan da kake a yau, me kake yi don tabbatar da wannan mafarkin naka?

Masu kyau ne?
Ko masu muni?
Ko a zaune kake kara zube?

Tabbas za ka girbe abin da kake shukawa ne a yau, a gobe. Idan ba ka shuka komai ba kuma, ba za ka girbe komai ba.

Ka sani!

Rayuwa ba ta kasance haka kawai, samar da ita ake yi. Haka Ubangiji ﷻ ya sunnanta rayuwa ta kasance, sai an yi wani, wani yake kasancewa. 

Ubangiji ﷻ shi ke halittar ɗan Adam, amma sai ya yi sanadin zuwan ɗan Adam ta tsatson mahaifa. Me ya sa ba a wullo ka daga sama ba?

Ubangiji ﷻ shi ne ke azurtawa, amma sai ya sanya wani aiki, ko kasuwanci su zame sila. Me ya sa kuɗi ba su zubowa daga sama kamar ruwa ko iska?

Ubangiji ﷻ shi ne yake shiryarwa, amma duk da haka sai da ya aiko da Manzanni عليهم السلام don yi ƙira zuwa ga shiriya.

Koda rayuwa ta zo maka da bazata, ba ka taɓuka komai ba, alheri ya riske ka... tabbas Ubangiji ﷻ ya sunnanta wani cikin ɗan Adam ya yi aikin ne a madadinka. Misali, iyayenka su mutu ka ci gado, ko wani Ubangidanka da ya yi gwargwamaya ya ɗan sammaka daga abin da ya tara.

Kana son babbar mota?
Kana son sutura irin ta wane?
Kana son gida irin na wane?
Kana son ɗaukaka irin ta wane?

Ba za su maka haka kawai a banza ba, ba tare da ka taɓuka komai ba. Koda za su zo, wani ne ya sha gumin a madadinka, kamar a misali na sama.

Kai me kake yi don cimma wannan ƙudurin naka a yau? Ba gaggawa, a hankali za ka gina kanka, kamar yadda ba a haka gwanɗamemen ƙato iyayenka suka haife ka ba, tun kana ɗan ƙarami kake girma a hankali, a hankali.

Kada ka damu don ka fara yau, shi ma wanda kake gani yake ba ka sha'awa saboda ɗaukaka ko kayan alatu da ya tara, ba yau da ya tashi daga bacci ba ne gan su, ya sha gwagwarmaya.

✍️Aliyu M. Ahmad
23rd Rajab, 1446AH
23rd January, 2025CE

#RayuwaDaNazari #AliyuMAhmad #AliMotives

Post a Comment

0 Comments