Kada ka taɓa tunanin wayonka ne, sai Ubangiji ya bar ka da wayonkan, ya ga ya za ka yi?
Kada kuma ka taɓa ganin wasu a matsayin marasa wayo. Ai da ilimi, da dabara, da damar, duk Ubangiji ﷻ ke kimtsawa bayi, a duk lokacin da ya so.
Mu dai nema ne namu, amma nasara da arziƙi duk na Allah. Ubangiji ﷻ ne kuma ya kimtsa hanyar nasara na tare da aiki.
Ka kiyaye wannan!
Kada saboda Ubangiji ﷻ ya buɗa maka ƙofofin arziƙi da wuri, sai kuma kake yi wa sauran mutane kallon ba su da wayo da dabara, malalata ne. Kana yi wa kanka kallon ai kai na musamman ne (entitlement).
Mutum nawa ne suka fi ka dagewa a irin hanyar da ka bi (ta nema) amma har yanzu ba su kamo ka ba? Mutum nawa ka fi hazaƙa, shekaru, asali... amma sun ɗara ka a tara abin duniya? Kamar a makaranta ne, a cikin ajinku, akwai waɗanda sun fi ka naci da dagewa da karatu, amma sai ka tsere su a GCPA. WAYONKA NE?
Morgan Housel a cikin Psychology of Money (2020) shafi na 33 yake faɗawa ɗansa, cewa "Ba dukkan nasara ce ke samuwa saboda jajircewa ba, ba kasala ke sabbaba dukkan talauci ba, ka kiyaye, ka sa wannan a zuciyarka, ka kuma kiyaye yanke wa mutane hukunci, ciki har da kanka".
Mutum nawa suka sami arziƙi daga baya suka talauce? Mutum nawa ne ba su da komai a jiya, amma a yau Allah ya sa suka zama abin kwatance? Mutum nawa suka tara dukiyar amma ta zame musu bala'i da jarrabawa? Mutum nawa ka riga samun aiki, amma yau sun ɗara ka da komai? Allah ke juya arziƙi, yake bayar da shi ga wanda ya so, a lokacin da ya so, ya kan sanya sila ne kawai, cikin aiki, wata sana'a, ko kasuwanci, ko ma connection, "DARE ƊAYA ALLAH KAN YI BATURE".
Kuma idan aka ce arziƙi, sai tunaninka ya taƙaita a iya kan iya kuɗi, kuɗi, kuɗi... haƙiƙa ka tsuƙe ma'anar arziƙi, sunan Ubangiji Ar-Razzaƙu (Mai azurtawa) shi ke arzuta bayi monetarily (da kuɗi ko dukiya) da kuma non-monetarily (ilimi, lafiya, kwanciyar hankali, mutunci...). Kada ka taɓa sakawa a ranka ka rako wasu duniya ne saboda ba ka kuɗi irin nasu, duk yadda ka kai hamshaƙi dole akwai abin da wani ya fi ka. Ka saurari nasihar da Luƙman ya yi wa ɗansa, cikin aya ta 12 zuwa ta 19 cikin Suratul Luƙman.
Always be humble! 😌
Kamar kiftawar ido, Ubangiji ﷻ zai iya ɗaukaka ka, haka nan a ƙasa da 1sec zai iya karya ka, a shafe labarinka kamar ba a yi ba. NAWA AKA YI?
✍🏻Aliyu M. Ahmad
3rd Dhul-Qidah, 1445AH
11th May, 2024CE
#AliyuMAhmad #AliMotives #RayuwaDaNazari
0 Comments