A YI SIYASA BA DA GABA BA!


Da yawanmu muna biyewa 'yan siyasa ne, domin maslahar kanmu, don mu samu rufin asiri. Ma'ana, in an kai ga nasara, a yi gwamnati da mu, mu ma mu sami romon da ake sharba, mu yi gidaje da abin hawa. Ina da tabbaci, 'yan siyasar nan da ace ba su da wani madafun iko, ko hasashen za su samu, da ko wurinsu ba za mu je ba.


A matsayinmu na Musulmi, MU YI SANI, arziki; Allah ke bada shi, dan Adam kawai sanadi ne. Tamkar yadda ka yi imani, Allah Shi ne ya halicce ka, amma ya yi sanadin zuwanka ta tatson mahaifanka.


Duk soyayyarka ga dan siyasa, ba zai soka kamar dan cikinsa ba. Amma baka tunanin, me yasa 'ya'yansa da za su fika morarsa, ba sa 'media' domin tallata mahaifinsu? Ba a jayayya da su domin su kare mahaifinsu? Ka fi su wahala, sun fi ka mora...


Ni dai ina kara bawa matasa shawara, kar soyayyarka ko goyon bayanka ga dan siyasa ta sa ka zubda mutuncinka, bata alakarka da kowa, ko ka yiwa wanda baka kauna kazafi, karya, habaici da yarfe. 


Ko abin arziki ne ya zo, offer (ta guraren aiki), ko kwagila, za a yiwa wadanda suka yiwa siyasa bauta, nutsattsu, masu ilimi da kamala ne ke cin gajiya; ba masu hauragiyya ba. 


Abu na karshe kuma, MUSULUNCI yana nan da tsarinsa, a cikin kowanne hali da yanayi, duk abin da ka aikata mai kyau, ko mai muni, da dukkan gabban jikinka, ko da tunaninka, na mu'amala ko aiki, kai hatta abin da kake kullawa cikin zuciyarka, sai an maka hisabi a kansa [Al-Isra', aya ta 37].


Akwai kuma rayuwa bayan zabe!

Allah Ya zaba mana mafi alheri🤲🤲


✍️ Aliyu M. Ahmad

5th Shawwal, 1443AH

6th May, 2022CE


#AliyuMAhmad #Siyasa #RayuwaDaNazari #RayuwaDaLissafi #Jigawa

Post a Comment

0 Comments