Kai!


Kai 🫵🏻

Ka tsaya, ka nutsu,
Ka gina kanka, don kanka,
Ka gina kanka, don iyayenka,
Ka gina kanka, don 'ya'yanka na gobe.

Amma ka tsaya kana ɓata lokaci,
Kana kashewa 'yan mata kuɗi,
Kana son burge 'yan mata.

Ka dai sani!
Mace ba da ta asara.

A yau budurwarkan nan, 
Ko ba ta da SISI, ba ta da KOBO, 
Ba ta da aikin yi, ko ba 'yar kowa ba ce... 
Za ta iya zama matar GWAMNA, ko wani HAMSHAƘIN MAI ƘUDI, a dare ɗaya a ɗaga darajarta.

Kai kuma fa namiji?
Ka sake nazari!

Idan ba ka shirya aure ba a yanzu ka fita sabgar 'yan mata. Gina manufa don gobenka ta yi kyau ya kamata ka yi, ba gina soyayya ba. Za ka gama yi wa yarinya hidima, wani ready-made latecomer zai zo, a ce ai ba ka shirya aure ba ne, kuma dole ka haƙura. 

Ka yi asara lokaci a banza.
Ka kashe kuɗi a banza,
Ba a YAUDARE KA BA, 
Kai ka YAUDARI KANKA.

Ka tuna, kai namiji! 

Musamman idan ka san babu mai tallafa maka, iyayenka na buƙatarka nan da 'yan shekaru; a lokacin da za su fara gajiyawa saboda shekaru. Nasararka hutunsu ce, akasarin haka, ƙasƙancinka har su zai shafa.

✍️Aliyu M. Ahmad
10th Rajab, 1446AH
10th January, 2025CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments