2025


Kowa ya iya faɗar: 

2025 shekarar cikar burina,
2025 na yi plan da kyau,
2025 zan yi kaza da kaza…

In faɗa maka gaskiya, 
Idan ba ka yi aiki ba, 
Ka ka yi amfani da lokaci yadda ya kamata, 

Duk wannan plans da burinka zai zama mafarki (dreams) ne. AIKI AKE YI DOMIN GANIN SAUYI A RAYUWA.

Faɗa a baki ya fi komai sauƙi,
Kowa zai iya faɗa a baki,
Amma aiki fa sai mutumin gaske.

Kuma ji!

Da 2024, da 2025 duk ɗaya ne, sai ga wanda ya canja kansa. Haka nan kowacce shekara ta iya zuwa da wasu damarmaki ko ƙalubale. 

Ta ya za ka sauya kanka?

1. KA FARA SANIN KANKA, KAI WAYE? (SELF-AWARENESS)

• Sanin kanka zai sa ka san me kake buƙata,
• Sanin kanka zai sa ka san me ya kamata ka yi.
• Sanin kanka zai sa ka iya bambance kai kanka, da kuma sauran mutane.

Abokinka da iyayensa ke iya yi masa komai, ba ɗaya kake da shi ba da kai da kai ne kake ƙoƙarin yi wa kanka komai. Don haka, burinku, da jajircewarku ba ta za ma ɗaya ba. Kai za ka nemawa kanka, shi kuma yana da gata, idan ka biye shi, kai ne a ruwa.

Sanin kanka zai sa ka fahimci ɗabi'unka daban suke da na sauran mutane. Sanin ɗabi'unka zai ba ka damar iya sarrafa kanka a wurare daban-daban, da kuma fahimta mutanen da ke kewaye da kai.

KA GANE KAI WA KAKE, SANNAN KA SAN INDA KAKE SON ZUWA! INA KA DOSA?

2. GINA MANUFA (GOAL)

Ka zama mutum mai manufa, ka zama mutum mai tsari da burin da kake son cimmawa a kullum. 

Me za ka yi a yau? 
Me kake son cimma a wannan sati? 
Wata? a Shekara? A rayuwarka gaba ɗaya? 

Wannan tsari na MANUFA zai fitar da kai daga rayuwar shagala zuwa rayuwar da ke da fa’ida da manufa. Model mafi sauƙi, ka koyi yadda ake gina MANUFA da BURI bisa tsarin SMART:

• S (Specific) = Mene ne takamaiman abin da kake son cimma?
• M (Measureable) = Wanda za a iya auna cigaba.
• A (Achieveble) = Wanda za a iya cimma, kada ka ɗauko abin da ya fi ƙarfinka.
• R (Relevant) = Wanda ya dace da manufa ko burinka a rayuwa.
• T (Time bound) = Wanda yake da lokaci takamaima da za a iya cimma.

A kullum kuma aiyukanka su yi daidai ko su yi alaƙa da ƙoƙarinka na cimma wannan burin naka. Rashin manufa ke sa hatta lokacinmu ba mu san me za mu da shi ba, sai mu riƙa ɓata lokaci a social media, kallon films, shagala... shi ya sa masu hikima ke cewa: "WITHOUT GOALS, ONE IS EASILY DISTRACTED BY PLEASURE". Rashin manufa ke sa matasa kule-kule 'yan mata da sunan soyayya, wasu shaye-shaye, wasu z^na, da sauransu.

3. KA IYA AMFANI DA LOKACI (TIME MANAGEMENT)

2024, 2025... duk lissafi ne na lokaci. Duk wani aiki da za ka yi, daga ibada zuwa aikin neman kuɗi, ilimi… ana yin su ne a cikin LOKACI. Kullum mutane suna ƙaryar BUSY, BUSY... sai ka rasa wacce uwa suke da lokacinsu saboda rashin TIME MANAGEMENT, da wani busy maras kawo KOBO.

A 2025 ka koyi ɗabi'ar shirya jadawalin aiyukanka na kowacce rana (TO-DO list/daily routine), tun daga lokacin tashi daga barci har zuwa lokacin bacci. Misali:

• 5:00am - 5:30am Tashi daga bacci/Sallar Asuba
• 5:30am - 6:00am Meditation/Adhkar
• 6:00am - 7:00am Karanta littafi/Exercise
• 7:00am - 8:00am Wanka, Breakfast da Sallar Dhuha
• 8:00am - Fita wajen aiki/Project I
• 10:00am - Project II, III....
• 1:00am Sallar Azahar & Launching
• 3:30am Sallar La'asar.....

Ka yi wa kanka tarbiyyar bin duk abin da ka ƙudurta, ka yi tattalin lokaci. Amma dole sai ka ajiye ko rage duk wani abu da zai sanya ka jinkiri gudunar da abubuwan da ka shirya, misali social media, ko hira, ko fita yawace-yawace marasa dalili. 

Ka gwada yin wannan na kwana 3 a karon farko, ka auna da yadda kake ɓata lokacinka a baya. Sai ka kuma ka sake yin na sati, wata, shekara... har ya zame maka al'ada, za ka fa'idanta sosai a rayuwarka.

3. KA IYA SARRAFA MOTSIN ZUCIYARKA (EMOTIONS)

Sanin yadda ake sarrafa motsin zuciya ya hada da abubuwa guda biyar:

a. Sanin kai (self-awareness) - Wannan mun yi bayani a sama.
b. Iya sarrafa kai (self-regulation) - Wannan ya haɗa da iya mallakar zuciya, gyara dabi'u marasa kyau...
c. Karfafa kai (self-motivation) - Ka iya ƙarfafa wa kanka gwuiwa kan cimma wani burinka, da fuskantar ƙalubalen rayuwa.
d. Iya mu'amala da mutane (social skills) - Ka fahimci ɗabi'un mutanen da ke kewaye da kai, yadda za ka yi mu'amala da kowanne, ba tare da sun cuce ka, ko cutar da su ba, ko sasantawa bayan kun sami saɓani da mutane.
e. Tausayi da jin kai (empathy) - Ka iya fahimtar yanayi da halin da wasu suke ciki.

Rashin iya sarrafa motsin zuciya ke sa ake bin son zuciya. Mutum sai ya bi sha’awa, gasa da wasu, ko ya zaɓi abin da yake so fiye da abin da ya fi buƙata. Ko ya cutar da kansa, ko ya cutar da waninsa.

4. KA KOYI YADDA ZA KA RIƘA TATTALI (PERSONAL FINANCE/FINANCIAL DISCIPLINE)

Yadda za ka iya sarrafa kuɗinka yana da muhimmanci don cimma burukanka na rayuwa. Personal Finance yana nufin kula, tara abin da za ka yi amfani da shi a gaba, shirya wa duk wani da zai iya tasowa na gaggawa, da gina financial goal na kashin kanka. Wannan ya haɗa kula da yadda kake:

a. Samun kuɗi (incomes), 
b. Kashewa (spending), 
c. Ajiyewa (saving), 
d. Zuba jari (investment), 
e. Karɓar bashi bisa buƙata da yadda za ka sauƙe nauyi, da kuma
f. Kare dukiyarka (protection) daga lalacewa ko asara.

5. KA KOYI HAƘURI DA JURIYA (RESILIENCE)

Ka sani, a rayuwar nan ba lalle ne duk abin da muke so su tafi daidai da yadda muke so. Ko da mu mun yi iya bakin ƙoƙarinmu akan iya samun 'external factors/forces' da za su zame mana shinge. Ka lura, duk wata rashin nasara tana tare da wani darasi maimakon ɓata rai da shiga damuwa, ka kula da darussan da matsalolin rayuwa ke koyarwa maka.

6. KA DAINA KWATANTA KANKA DA SAURAN MUTANE

Duk wanda ke son ci gaba ba ya ɓata lokaci yana kwatanta kansa da wasu. Wannan yana sa ka kasa lura da ci gaban da kake samu. Saboda a kullum za ka ga kamar ba ka komai saboda kana kwatanta kanka da waɗanda suka fi ka nasara da ɗaukaka.

5. KA GINA ƊABI'AR CI GABA DA KOYA (CONTINUOUS LEARNING)

Ilmi ba ya karewa, ka ɗauka rayuwa makaranta ce da za ka riƙa koya a kullum. Za ka iya koyon rayuwa daga wanda ka fi shekaru, ko ilimi ko wani matsayi. Kada ka ɗauki kanka ka san komai.

6. KA GINA KYAKKYAWAR DANGANTAKA DA MUTANE (NETWORKING)

Babu wanda zai iya yin komai shi kaɗai. Ka nemi mutanen da za su taimaka maka da shawara, ilmi, da kuma ƙarfafa maka kwarin gwiwa. A kullum kana kula da mu’amalar da kake yi da mutane. Ka koya yin magana da mutane a cikin natsuwa da nuna girmamawa ga kowaye. 

A ƙarshe mu sani, rayuwa gina ake, ba jiran faruwarta ba. Ko tsuntsu da ake buga misali da shi kan tawakkali (dogaro da Allah) a kullum, kowacce safiya sai ya fita ya nemi abinci. Tsuntsu dabba ma kenan, ina ga kai ɗan Adam? Allah ya taimakon wanda ya jajirce ya riƙe sababi koda ba Musulmi ba ne.

 ✍️ Aliyu M. Ahmad 
1st Rajab, 1446 AH
1st January, 2025 CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments