Wait! 🤔
Akwai wani abu guda 1 da muke mantawa, sau da yawa muna yawan maganar:
A yi karatu,
A koyi skills,
A sauya tunani,
A iya amfani da AI,
A tafi da zamani...
Wannan a baki ne (magana),
Ko a rubutu,
Kowa zai iya saurara,
Kowa zai iya karanta,
Amma kowa ne zai iya sauyawa?
Kowa ne ya san ta ina zai fara koya?
A'a,
Mutane da yawa suna son su sauya, a halayyarsu, upskilling kansu, amma ba su fa san yadda za su fara yi ba.
Cikin (kai da ni) masu rubutu ko magana, ka/na taɓa shirya 'trainining' da zai 'impacting' mutane kan abubuwa da muke yawan advocating mutane/matasa su yi ko su sauya?
A shirin sauya kai da tanadi, mun shirya tafiyar kwana 50, #Vision2025 (da participants kusan 200), wanda a yanzu mun yi kusan kwana 40 da farawa, kwana 9 ya rage mu ƙarƙare.
Daga cikin horon sauya tunani da tanadin rayuwa:
1. Mun fara koyar yadda ɗan Adam zai san kansa, ta fuskar ɗabi'a da halayya bisa ma'auni Tim LaHaye (1926 - 2016), FOUR TEMPERAMENTS (Sanguine, Choleric, Melancholy da Phlegmatic).
Da fahimtar waɗannan halayyar a tattare da mu, da kuma waɗanda ke kewaye da mu. Tare da sanin iyakokin (kicas) da kowanne cikin waɗancan halaye za su iya kawo mana a rayuwa, da damarmakin da halayenmu za su iya samar mana a rayuwa. KOWANNE ƊAN ADAM YANA DA RAUNI, ya kuma ƘARFI ta wani ɓangare, KOWAYE!
Sannan mun yi karatu a kan ƙima (value), da kaɗan cikin baiwa (intelligence) da yadda suke tasiri a rayuwa. Sannan muka haɗa da wajabta karanta littafin 'KA SAN KANKA' na Ahmad Sani don ƙara fahimta 'tempraraments'.
2. Mun koyar da yadda ake gina manufa bisa ma'aunin SMART GOAL na George T. Doran (1981).
Mun haɗa yadda ake gina MANUFA da BURI bisa SMART:
• S (Specific) = Ƙayyadadde.
• M (Measureable) = Wanda za a iya auna cigaba.
• A (Achieveble) = Wanda za a iya cimma.
• R (Relevant) = Wanda ya dace da manufa ko burinka a rayuwa.
• T (Time bound) = Wanda yake da lokaci takamaima da za a iya cimma.
3. Mun yi karatu kan TIME MANAGEMENT (iya sarrafa lokaci), tare da models 10 na TM:
• Eisenhower Matrix,
• Pomodoro Techniques,
• GTD,
• Pareto Principle (80/20 Rule),
• Time Blocking,
• ABC,
• Parkinson's Law,
• 4D System,
• 2-Minute Rule da
• Eat That Frog.
Tare dabarun sarrafa lokaci ta hanyar amfani da wasu manhajoji na wayar hannu, ciki har da Google Digital Well-being, Facebook Timer, Microsoft To-Do. Mun kuma wajabta yin DAILY ROUTINE/TO-DO LIST kullum, tun ranar fara darasi.
4. Mun yi karatu kan EMOTIONAL INTELLIGENCE da DARK PSYCHOLOGY don fahimtar motsin zuciyarmu da na waɗanda suke kewaye da mu.
Mun koyar da yadda za mu iya sarrafa kanmu cikin yanayin ɓacin rai ko farin ciki, ko kuma martani daga munanan halayyar wasu mutane da triggers nasu.
5. Mun yi wa kanmu karatun kan PERSONAL FINANCE, da yadda za mu iya gane me yake shiga da fita daga tattalinmu arziƙinmu. Mun duba Praymid of Priorities, wajen kashe kuɗi tare da wasu dabarun kasafta kuɗi (budgeting) na 50/30/20, PYF, ZBB, Evelope System, da sauransu.
6. Mun horar da kanmu kan MINIMALISM cikin rayuwa, tattali, motsin zuciya, amfani da lokacin, mu'amala da mutane, wadatar zuci... da sauransu.
7. Abin da ya rage mu ƙarƙare Digital Well-being ne, darussan cikin kuskuren rayuwa da kuma self-reflection.
8. Tun fara shirinmu na Vision 2025, mun wajabta karanta abin da bai gaza shafi 10 ba na littafi a kowacce rana (a kullim). Daga cikin littafan da muka karanta 'so far' akwai:
• Ka San Kanka na Ahmad Sani
• Tunaninka Kaminka na Bashir Tofa
• Wane ne Bahaushe na Aliyu M. Ahmad, sai kuma
• Tarbiyya na Prof. Dogarawa
SAUYI ko CANJI ba fa a iya baki ba ne, AIKI ne. Ba kula aikin rana 1 ba ne. Duba yadda Ubangiji ﷻ ya wajabta azumi na kwana 30 don mutane su sauya rayuwarsu, duba yadda muka sanya wa kanmu kwanaki 50 don sauya tunani da kuma cimma wasu burikanmu a 2025.
Ba kawai rana 1 ba ne ake ake sauya, kuma Ubangiji ƙara ya faɗa mana, إن الله لا يغير ما بقوم حتى يغيروا ما بأنفسهم, ma'ana "Ubangiji (fa) ba ya sauya al'umma har sai wannan al'umma ta sauya abin da yake kanka (na tunani, ɗabi'a da aiyuka).
Na biyu, idan mun so da kuma ƙaunar ganin mutane da ke kewaye da mu sun sauya, ba a iya baki ba ne za mu faɗa, ko mu rubuta su karanta kawai, a'a; mu ja su a jiki, mu nuna musu. Idan ma mu ma ba za mu iya ba, mu jawo ko gayyato masana su koya musu, gyara halayya ne, ko koyon wani skills, digital ko vocational skills ko da koyon harshen Turanci ne don amfanin gobe.
Bayan ka ba da shawara mutane su sauya ko su koyi abu kaza da kaza, wane yunƙuri kuma ka yi don ganin sun sauya ko koyon? Yi koyi na Muhammad Auwal Ahmad da Flowdiary, ga Ahmadun Gumel da Turnup Jigawa. Kowa zai iya da abin da yake da shi na basira, tattali ko ilimi.
✍️Aliyu M. Ahmad
20th Jumaada II, 1446 AH
22nd December, 2024 CE
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives
0 Comments