Ka Waiwaya!


Kada wani ya ce zai iya abu kaza a 2025, ya kuma yi niyyar canza hali, alhali bai tambayi kansa ba: 

"A 2023 ma na yi irin wannan niyya da alƙawari, amma ba abin kirki na yi ba a 2024." Don haka, tambayi kanka: 

"Ina matsalar take?", 
"Mene ne ya hana ka cimma burinka a 2024?", 
"Mene ne ya hana ka maida hankali?".

Ka dai sani! Abin da ka shuka, a kullum akwai tabbacin 99.9% cewa shi za ka girba. Ɗaiɗaiku ne ke faɗowa cikin 0.1% saboda wasu 'external forces' da suke iya pushing mutum ya samu nasara ta dalilin wasu mutane.

✅ Ka ɗaura niyya.
✅ Ka riƙe sababi.
✅ Ka yi abin kirki.
✅ Ka yi addu'a.
✅ Allah zai taimake ka.

Ba komai ake jingina wa ƘADDARA don ka nema wa kanka UZURI ba, domin Allah ya yi maka baiwa, ya ba ka hankali, tunani da lafiya. A duniya, 100% na alhakin kula da kanka yana kanka ne, sai dai idan kai ƙaramin yaro ne wanda bai kai ga balaga ba (alhaki kulawarsa na kan iyaye ko waliyansu).

Tsuntsu da ake ba da misali da tawakkali, kullum sai ya fita neman abinci. Aljannar da da rahamar Allah ake shiga, amma rahamar nan tana zuwa ne ga waɗanda suka yi aiki na gari ne. Ubangiji kuma ya yi alƙawarin taimakon waɗanda suka ƙoƙarta a duniya da lahira.

Ka dage. 
Ka yi iya ƙoƙarinka. 
Allah yana tare da masu ƙoƙari.

A kullum dai, abin da shuka, shi za ka yi tsammanin girba, a duniya da lahira; na sharri ko alheri, na kasala da lalaci ko ƙoƙartawa da sadaukarwa. Aiyukanka na yau da kullum za su iya zame maka sanadin samun sa'ida a duniya ko lahira.

✍️Aliyu M. Ahmad
24th Jumaada, 1446AH
26th December, 2024CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments