Kai ɗan talaka!
1. Ba ka da wani gata ya wuce ka tsaya ka GINA KANKA. Ka sanya manufa a rayuwarka, ka ƙuduri aniyar cimmama wannan manufar, kowacce ce.
2. Ka iya gane rauninka (weaknesses) da abin da za ka iya (strengths), ka sanya idonka kan damarmakinnda suke gabanka (opportunities), da kuma wane irin ƙalubale za ka fuskanta wajen cimma wannan manufarka (threats).
3. Ka toshe kunne daga kowanne abu da zai kashe maka gwuiwa, ba wani abu duniyar nan da ba shi da ƙalubale. Ka guji sauraran sautaka masu kashe gwuiwa. Ka nemi wanda zai iya taimaka maka ka cimma manufar idan ka gaza, cikin 'yan uwa, ko iyayen gida (kai dai ka iya mu'amala, jari ce).
4. Idan ka sami damar yin karatu ka yi, "لا فقر بعد العلم", duk abin da ka karanta zai yi maka amfani, a ofis, ko a karan kanka za ka iya monetisation nasa. Idan ba ka sani ba ka tambayi masana su saka ka a hanya.
5. Idan sana'a kake, kada ka ji ce wa aikin ofis ya fi naka. Da mai aiki a ofis, da mai yi a bakin hanya, da na gareji... kowa fafutukar yadda zai rufawa kansa asiri yake yi. Kai dai yi ƙoƙari da tunanin yadda a kullum za ka bunƙasa, YAU TAFI JIYA, GOBE TAFI YAU.
6. Idan kana sha'awar aikin ofis ko kamfani, ka yi karatu da kyau, ka sami kyakkyawan sakamako (certificate), ka yi addu'a, nemi sanadi da sila (connection).
• Akwai abokina da muka yi secondary tare shekara 6, muka ci gaba da karatu tare a Legal, shekara 2. Da kwalin Diploma a Qur'anic Science ya samu aiki a Central Bank of Nigeria (CBN). Daga 2015 zuwa yau, yana gida da iyali, asirinsa a rufe, ya ma rufawa wasu.
• Akwai kuma mutumin da na sani, ya ajiye aikin lecturing, ya koma aikin mining tare da wasu 'yan China a jihar Taraba.
• Akwai labarin wanda na taɓa wallafa a wannan shafin, ya dage ya yi boko da kyau, ya sami aiki mai kyau, yanzu yana ƙasara China yana MSc da scholarship.
• Akwai wanda a sahar nan, yana cikin friendlist nawa, a cikin wata 1, ya sami offers guda 6, cikin har da Lagos da Abuja, ya zaɓi guda ya tafi.
• Akwai wanda ya yi nasara a kasuwa, wani a noma, wani a siyasa, wani a aikin birkilanci, wani tela, wani shi yake yi gwamna aski. A komene ne za ka iya nasara, idan ka sa gaba, ka yi aiki tuƙuru, Ubangiji ya shige maka gaba.
SAI DAI KA JI! BA WANDA NASARA TA ZO WA A RANA 1, TANADINTA AKA YI, SHIRYA MATA AKA YI... HAR ALLAH YA KAWO TA.
7. Kada ka taɓa tunanin don ka taso gidan masu ƙaramin ƙarfi kai ma a haka za ka ƙare cikin ƙaramin ƙasƙaci a idon mutane. Ka duba asalin duk mutanen nan da ake yi wa jiniya (siren), 'ya'yan su waye? Sai ɗaiɗaiku ne iyayensu gawurtattu, yawanci FROM GRASS TO GRACE ne, kai ma za ka iya zama fiye da tsammaninka.
Ka cire kasala,
Ka gina kanka a karatu da kwarewar aiki,
Ka yi addu'a,
Ka yi sabo da maza (gina connection),
Ka yi mu'amala mai kyau da kowa,
Ka jira lokaci.
✍️Aliyu M. Ahmad
6th Dhul'Hijjah, 1445AH
12th June, 2024CE
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives
0 Comments