Social Media Addiction


Abin ci ne fa, za ka iya ci a 10 - 20mins, amma sai ka fi 1hr kana zaune kana ci, saboda ka riƙe waya a hannunka, kana cin abinci, kana scrolling social media.

Fitsari wannan (ka tsugunna ka tashi), da za ka yi 5 mins ka fito a bayi (toilet), sai ka ɓata sama da 30mins a tsugunne, saboda kana scrolling feeds a wayarka.

Aikin da za ka iya kammalawa a 1hr, sai ya ɗauke ka 3 - 4, duk saboda ka kana scrolling feeds a waya.

Da ka tashi a bacci, ba ka kya iya sauƙa a kan gado ko shinfiɗa, ba ka iya miƙewa sai ka ɓata 30mins, 1hr, 2hrs... duk saboda waya.

Salla za a iddar a masallaci, maimako ka fara zikiri sai ka ɗauko waya kana buɗe WhatsApp, Facebook, TikTok... Kai ka ce wani abu za a yi ba ka nan, ka ɗora wa kanka FOMO.

Kuma ka zo kana cewa lokaci yana gudu, ba ka san inda kake ɓata lokacinka ba ne? Kuma babu wata tsiya, kuɗi ko value da scrolling ke kawo ma rayuwarka sai ɓata lokaci.

Karfi da yaji ka sanya wa kanka cutar kasala/nawa (proscrination), har social media addiction ya kama ka ba ka sani ba.

✍️Aliyu M. Ahmad
12th Jumaada II, 1446AH
14th December, 2024CE

#RayuwaDaNazari #AliyuMAhmad #AliMotives

Post a Comment

0 Comments