Kafin ka ɗora wa ƙaddara,
Kafin ka zargi kowa kan damuwarka,
Ka fara duba aiyukanka na jiya,
Ka fara duba aiyukanka na satin da ya wuce,
Ka fara duba aiyukanka na wancan wata,
Waccar shekara da taa wuce,
Shekaru 2, 3, 4, 5... da suka wuce.
Duk suna da alaƙa da halin da ka tsinci kanka a yau.
Cewa ƙaddara ce,
A'a, laifin wasu mutane ne,
Duk kanka kake nemawa uzuri,
Na kasalarka,
Wawan zaɓinka,
Biye wa son zuciyarka.
Yanzu kuma kake girbe shukar da ka yi.
Sunnar rayuwa ce,
Ba Musulmi ko waninsa,
Ba mutum kirki, ko na banza,
Ba babba ko yaro,
Ba mace ko namiji.
Duk abin da kake aikatawa a yau, shi ka tarar gobe, ko shekaru masu zuwa, har a lahira.
Kana da damar sauƙa a wani layi na kuskure don ka gyara gobenka, ka RAGEWA kanka ƙalubale da matsaloli. Ubangiji ﷻ na taimakon wanda ya yi kataɓus ne, ba malalaci ko mai bin son zuciya ba.
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives
0 Comments