Sabuwar Shekara 2025


Na sake faɗa, SABUWAR SHEKARA ba ita za ta sauya ka ba, kai ne za ka sauya kanka. 

• Kada ka yi zaton idan kana aikata wani mummunar abu/aiki, wai idan 2025 ta shigo za ka daina. Ƙarya kake yi wa kanka Malam!

• Kada ka yi zaton sai 2025 ta shigo za ka fara koyon wani skill(s). Ƙarya kake yi wa kanka matuƙar ba ka fara shiri a yanzu ba.

• Kada ka yi zato da 2025 ta shigo rayuwarka za ta sauya. In faɗa maka rayuwar nan cike da ƙalubale, idan za ka ware ma, ka tashi ka fara shiri a yau.

Ranar 1 ga watan Janairu, 2025, kamar sauran ranaku ce, ba ita za ta zo da sauyi, rana ce kamar kowacce rana da take zuwa da alheri ko sharri ga kowa. Ubangiji ya yi maka basirar ka zaɓa wa kanka rayuwa.

Sabuwar shekara bata nufin sabon sauyi, a'a, ita ma rana ce kamar sauran ranaku da kake rayuwa.. An sanya mana lissafin rana da wata ne domin sanin lokutan da za mu rinka gabatar da wasu aiyuka na ibada, bukukuwa, tafiye-tafiye da sauran al'amuran yau da gobe [Suratul Isra' aya ta 12].

SHEKARA BATA CANJA KOMAI, 
SAI IN KAI KA CANJA KANKA.

Idan kuwa kana buƙatar ganin sauyi a rayuwarka, ko cikar wani buri naka, daga waccar shekarar zuwa wannan, sai fa ka yi huɓɓasa da gasken gaske... tare da haɗawa da sinadaran jajircewa, haƙuri, addu'a da neman shawarwari.

Duk wanda ka ga ya girbi wani abin alheri/kirki a 2024, ya yi shuka ne tun a 2024. Ɗaiɗaiku ke iya tsinka daga gumin wasu ne. Malam! Abin da ka shuka, shi za ka girba.

Fatan alheri!

✍️Aliyu M. Ahmad
30th Jumaada I, 1446AH
Mon. 2nd December, 2024CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments