Manufa


Wani zai ce, sai da ya fara gina gida (na kansa), sai ƙofofin alheri suka fara buɗe masa.

Ji! 

Manufa ce ka sa a gaba (a yanzu), shi ya sa ka ƙara azama da ƙarfafa wa kanka gwuiwar nema.

Wani ba ya maida hankali da zafin nema sai bayan ya yi aure. Lokacin ya san akwai nauyi a kansa, zai maida hankali, ƙofofin alheri su ƙara buɗewa.

Duk wata nasara da za ka samu bayan wasu shekaru a gaba, suna da alaƙa da aiyukan da kake yi a yau. Komai yana 'connecting-dots' ne.

Sau da yawa manufa muke rasawa a rayuwa, shi ya sa muke kame-kame. Ba ka san ya za ka tattala lokacinka ba. Babu dabarun shigowa da sarrafa kuɗi (financial literacy) a ilmance ko a aikace. Ba ka san me za ka yi a gobe ko shekara mai zuwa ba. A taƙaice dai, kara zube kake zaune, ba ka da wata manufa.

Amma da za ka sanya manufar cimma wani abu a rayuwarka, kai kanka sai ka fi maida hankali a rayuwarka bawan Allah. Kullum tunaninka, da aiyukanka, da zamarka da ƙarin gwuiwarka duk za su karkata kan yadda za ka cimma wannan manufa ne. Ya angwaye suke yi idan an kusa aurensu?

Manufa a rayuwa na da matuƙar muhimmanci. Yana ƙara wa mutum kwarin gwiwa don cimma burin da aka sanya a gaba. Idan mutum yana da manufa, yana da ƙara azama wajen fuskantar kalubale da tsare-tsaren rayuwa. Yana sanya mutum ya mai da hankali kan abin da yake nufi da kuma yadda zai samu nasara a wannan abun.

A sanya wata manufa,
Ka yi aiki tuƙuru don cimma ta,
Ka nemi taimakon Allah, saboda akwai ƙalubale da sauran external factors.

✍️Aliyu M. Ahmad
1st Jumaada I, 1446AH
3rd December, 2024CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments