Muna da gaggawar sharhi kan rayuwar mutane ba tare da mun san dalili da ya sa wasu ke irin rayuwar da suke ba.
Misali:
• Za ka iya zargar mutane ba su da aikin yi, bayan ga aiyukan yi nan kaca-kaca, amma ba ka san wani tun wayewar gari yake gararanbar neman abin yi amma bai samu har yamma. Sauran damarmaki da kake tunanin za a samun kuɗi da su, shi kuma ba shi 'skills' na su.
• Za ka iya zargar abokan karatunka na sakandire sun ƙi ci gaba da karatu a jami'a alhali ba ka san abinci (1/2 square meal) ma da kyar suke iya samu su ci, balle a tara kuɗi karatu.
• Za ka iya cewa wance ta shekara 25, 30... a gida ba aure, amma ba ka iya kawo mata mijin da zai aure ta ba (na gaske).
• Za ka iya cewa abokinka yana samun kuɗi ya fiye maƙo, ba ya ɗinka sutura kamar kai, alhalin kuɗin da yake samu mahaifansa yake ciyarwa da sauran ƙannansa marayu.
• Ba ka san dalilin da ya sa wani ya gaza ɗaukar ɗawainiyyar jinyar mahaifinsa ba, kai kuma ba tallafa masa za ka yi ba.
• Ba ka san dalilin yawan cin bashi da abokinka ke yi ba, kai kuma ba kuɓutar da shi za ka yi ba.
• Ba ka dalilin rabuwar auren wasu ba, duk da sun shaƙu da juna, sun yi auren soyayya.
Idan ba ka san yanayi da halin da mutane ke ciki ba, ka guji sauri da gaggawar yanke musu hukunci. Idan ma ka yanke musu hukunci, za ka ba su mafita ne? Wani lokacin ba ka iya gane yanayin da mutane ke ciki har sai ka tsinci kanka a ciki. Kai ma ka ji da naka matsalolin, ka kauda kai daga rayuwar mutane.
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives
0 Comments