Ka Ga Mace


Bari na biya maka karatu.
Ka gane bambancinka da mata.

Ka ga MACE! 

Allah ya yi mata sassaucin rayuwa da yawa, ba kamar na kai NAMIJI ba, da kai za ka kula da kanka, ka kuma ɗauki ɗawainiyyar wasu, da akwai, da babu.

Misali, ƙanwarka da mahaifinku ya rasu ya bar ku kake kula da cinta, da shanta da sauran buƙatunta. Ya zamana da kai ta dogara saboda kai ne yayanta na miji.

Ta fuskar tattali, tana ƙasa da kai. Amma in faɗa maka, a dare ɗaya sai ta iya ɗara ka arziki idan wani hamshaƙi ya zo ya ƙulla aure da ita, zai maida ta matsayi na sama.

Kamar haka ne idan LATE COMER ya zo ya rutsa ka, budurwaka da 'airtime' da 'data' ma kai kake ba ta, haka za ta yi sama ta bar ka da cizon yatsa. Budurwarka ba ta da asarar ko sisi, ajinta ne ma zai ƙaru idan mijin da za ta aura ya ɗara ka a aji (class).

Mace ba ta sakandire balle digiri,
Ba ta da ko sisi (na kuɗi),
Iyayenta ba kowa ba ne a gari...

Dare ɗaya za ta iya hawa ajin sama sanadiyyar auratayya. KAI KUMA FA ABOKINA?

Ka tsaya ka gina kanka,
Ka sanya wa rayuwarka manufa,
Babu wanda zai ji tausayinka don kana 'broke',
Babu macen da za ta so ka ba ka da sisi.

Ah to! Gaskiya magana kenan.

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments