Matashi Ka Lura!


"Hafiz, na ji an ce an yi auren budurwarka, ko shi ya sa nake ganinka a bayan layin can wajen Halimah?"
"Eh! Ai yau kusan 6 weeks, an kai ta Kano"
"Na ga shekararku 2 kuna soyayya, yaudararka ta yi kenan?"
"A'a, kutse kawai aka min, wani cousin É—inta ne ya zo daga Kano a shirye da niyyar aure, aka ce an ba ni dama na fito, idan kuma ba aure zan yi ba kada na É“arar mata damarta"
"Yanzu mene ne matsalarka?"
"KuÉ—i!"
"Amma tunda matsalarka kuÉ—i ce, kuÉ—i za ka nema ai ba wata budurwar ba, heal first! Amma sai na ga ka koma crushing wata yarinya a bayan layin can. Hala ka shirya ka ci gaba da kashe kuÉ—in 'airtime' da lokacinka, ka reni soyayya wani ya zo ya sake maka kutse?"

Kana matashi, kana tsaka da soyayya da budurwa, sai 'late comer' ya zo ya raba ka da ita, wane darasi ya kamata ka É—auka? MECE CE MANUFARKA DA SOYAYYAR? Rage lokaci, ko aure?

Da shirmenmu matasa sai mu sake faɗawa wata soyayyar, maimakon ka san kuɗi ka fi buƙata ba biye-biyen 'yan mata ba. Ka zo wajen DIJE, WANI ya aure ta saboda baka da halin aurenta. Ka koma wajen MOMY, UMMI, RAMSY duk dai abu ɗaya; maimakon ka yi tunani neman sana'a sai kuma kake ƙoƙarin neman soyayya da ANSATU kuma? Haba Guy!

Sha'awa tana kashe goben matasa da yawa, a ƙi maida hankali kan gina gobe, ya tsaya shirme da shirita suna dagula masa lamura. KUSKURE SAU ƊAYA AKE A RAYUWA, IDAN KUMA AKA MAIMAITA DA GANGAN YA ZAMA GANGANCI KUMA.

Mece ce manufarka da soyayyar? 
Rage lokaci, ko aure?

Ka je 'yan matan nan!
'Yan mata ba za su ƙare ba,
Kai na miji ne, ba za ka tsofe ba,
Matuƙar akwai kuɗi a lalitarka.

✍️Aliyu M. Ahmad 
5th Dhul-Qi'dah 1445 AH
14th June, 2024 CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments