Kada ka taɓa fassara nasararka da ta wani, ko ka fassara nasarar wasu da taka.
Misali:
Arziƙi (wadata), ba kuɗi kawai yake nufi ba. Nasara (success), ba tara kuɗi kawai take nufi ba. Taƙaita nasara ga kuɗi (kawai), kamar an tsuke ma'anar nasara da wadata (arziƙi) ne.
Idan a yau, buƙatata ta na samu ₦10k ne, kuma na samu ₦10k a yau, to na yi nasara a yau. Idan kai kuma a yau, buƙatarka ta ka samu ₦100k ne, amma sai ka samu ₦70k ko ₦90k, ba ka yi nasara ba. Ni mai ₦10k (if success is personal) na fi ka nasara.
Kamar masu jinya ne, wani ₦5 million ake nema a yanzu za a yi masa aiki a asibiti, za a kashe sama da ₦5 million, a yi aiki, kuma ba a yi nasara ba. Wataƙila kai jinyarka tun daga test, zuwa 'meds' ba a kashe ₦5k ba, kuma ka sami lafiya, an yi nasara. KOWA NASARARSA DABAN!
Wani nasararsa a yau, ya zama babban SIFETON 'YAN SANDA ne, wani kuma KURTUN 'YAN SANDA. Wani ya yi nasara a yau idan ya sami admission a jami'a, wani kuma nasararsa a yau a ɗaga likafarsa daga ASSOCIATE zuwa matakin cikekken FARFESA.
Wani nasararsa ya zama GWAMNA, wani kuma nasararsa idan gwamna ya shiga ofis ya ba shi muƙamin S.A. ko commissioner, kuma duk sun yi nasara.
Idan kawarki ta yi aure a shekara 18, ta yi nasara. Idan na ki auren ya zo miki a 25, 30... ke ma kin yi nasara. Mafi kyan nasara a aure walwala da kwanciyar hankali.
Za ka raina salary na ₦20k ko? Yanzu haka wani a yana neman aikin koyarwa a wata private school don ya riƙa samun wannan ₦20k a wata, kuma an ce masa ba sa buƙatar ma'aikata, har sai ya ji ƙunci a zuciyarsa saboda bai yi nasara ba. Kamar haka wani ya je bidding na neman kwangila da zai iya samun ribar miliyoyi ko biliyoyi ₦aira, kuma bai samu ba.
Matsahi!
Ka fitar da GAGGAWA a sabgarka.
Ka bi komai a hankali, mataki-mataki.
Abin da wani ya samu a shekara 5, kai wataƙila sai ka shekara 10, wani kuma sai ya shekara 20, wani kuma a shekara 1 ko 2. Ka bi komai a hankali, matuƙar kana kan layi, lokacinka zai zo, kuma duk kun yi nasara.
Kada ka saka wa kanka damuwa sai ka sami nasara irin ta wanda ya fara shekara 5 ko 10 kafin kai. Akwai faɗuwa, akwai kuskure. Idan an faɗi tashi ake yi, idan an yi kuskure gyarawa ake yi a gaba.
Ba gaggawa,
Ba 'shortcut'.
Manya masu kuɗi, ma'aikata da 'yan kasuwa da kake sha'awar rayuwarsu, suturarsu, motarsu da gidajensu, a lokacin da suke irin SHEKARUNKA ba su kai wannan matsayin ba, a hankali suka ginu, har suka kai wannan matsayi. Wani kuma yana arziƙin fiye da kai tun yana ƙasa da shekarunka, wannan kuma lamarin Ubangiji ﷻ ne.
Kuskure ne ka riƙa kallon mutane a matsayin MARASA NASARA, saboda ba su yi masara irin taka ba, don kana da basirar karatu, ko ka kai wani matakin karatu, ko samun wata dama, ko tara dukiya... kai ma ƙasan nasarar wani kake (idan ya kallo na ƙasa da shi). Kuskure ne ka ji ba ka yi nasara ba a rayuwa, saboda ba ka zama irin wani ba. Malam! Ka san me kake buƙata, me kake da shi a yanzu; sai ka yi wa Allah godiya.
✍️Aliyu M. Ahmad
21st Jumada I, 1446AH
24th November, 2024CE
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives
0 Comments