Ƙanina



Kai kam 'ƘANINA' ba dogon bayani zan maka, amma ka sani, a shekarunka 15, 18, 25... ba 'yan mata kake buƙata ba, GINA KAI ya kamata kafi maida hankali, karatu, koyon sana'a ko aikin dogaro da kai, iya zaman duniya...

Sha'awa ce ka tashen balaga kawai suke fizgar ka, kai a dole sai ka yi budurwa, sai ka yi soyayya, saboda zuciyarka ta fara motsawa. Daga nan tunaninka sai ya koma, ta ya za a yi ka fara burge 'yan mata, kuma ba ka da sisin kirki (ba ka tsaya da ƙafarka ba).

Daga nan za ka fara ƙoƙarin sai ka bi yayi (trends), don kawai ka nuna wa 'yan mata kai ma ɗan zamani ne. Sai kwaliyya, wayar hannu, ɗora wa kai hidima ma 'yan mata. Kana 'broke', kana son nuna wa 'broke' yarinya kai ba 'broke' ba ne. Iya 'airtime' na waya ma, kana iya kashe ₦1k, ₦2k... a kullum, for what?

Da za ka maida hankali, ka gina kanka, ka tara wa kanka value (ƙima), 'yan matan ne za suna nemanka, ba kai ne za ka neman su ba. Wasu kuma iyayensu ne za su riƙa son haɗa zuri'a da kai, saboda kana ƙima da mutuncin a cikin al'umma. Shi ne abin masu hikima ke cewa, "DON'T CHASE, ATTRACT".

Wani abun haushi, da za ka ɓata shekara kana soyayya da HAJARA, ta kai munzalin aure, aka ce ka fito, ba ka shirya ba. Wani, 'latecomer' ya zo ya doke ka. Maimakon ka yi hankali, ka gyara kuskurenka (ka yi ƙoƙarin nema wa kanka 'capacity'), a'a; sai ka ƙara neman soyayyar HAJJO don huce haushi 🤔 Haba!

Duk fa karatu da shawarar da ba za ka ji ba, har sai duniya ta yi maka, akwai matsala. Duniya ba ta karantar da mutum darasi, sai ta jajjage shi.

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments