Babu wanda ake cuta da tunanin nuna fifiko ko ƙasƙacin DIGIRI ko AIKIN GWANATI, da kuma SANA'A/SANA'O'I irin matasa masu tasowa (18, 20 - 25).
Dama can an tasowa BA A SAN INDA AKA DOSA BA, babu wata manufa a rayuwa (sai ta ci, a sha kawai a rayuwa), babu MENTORSHIP, ga yanzu kuma kuna rikitawa yara tunani, sun kasa samun nutsuwar me za su kama don su tsaya da ƙafarsu su tsira da mutuncinsu a gobe.
Ƙanina!
Ka toshe kunnenka daga RUƊUN 'YAN MEDIA. Ilimi shi ne matakin farko. Ba a fara ma Manzon Allah ﷺ wahayin isar da saƙo ba, sai da aka aka sauƙar masa da "اقرأ", ma'ana "YI KARATU!".
• Idan ka samu damar ka yi karatu, ka yi ƙoƙarin ka fahimci yadda za ka applying wannan ilimin don warware matsalolin duniyar zahiri, ka samu abinci. ZA KA IYA HAƊA KARATU DA SANA'A
• Idan ka samu damar yin karatu, ka yi ƙoƙarin koyon wani skills da za ka dogora da kanka, kada ka kwallafawa ranka aikin ofis/gwamnati.
• Idan ba ka samu damar samun karatun zamani mai zurfi ba, ka riƙe sana'a, kuma kada ka bari hassadar ba ka da digiri ta sa kana kashe wa wasu gwuiwa. Ina da tabbacin idan ka yi kuɗi, har ƙasar waje za ka biya tuition mai tsada don 'ya'yanka su mallami shedar DIGIRI.
Amma kai ba ka da DIGIRI,
Kuma ba ka wani KUƊI,
Ko wata SANA'A ta kirki,
Ba ka ma san ina ka dosa ba a rayuwa ba, amma kana gaba-gaba wajen faɗawa mutane mene ne ya fi wani kawo wa mutane mafita.
Ka ji!
A komai na rayuwa akwai ƊANGOTE, a sana'a, a karatu, aiki... Duk ƙanƙantar da sana'ar da ake rainawa, akwai wanda ya girma a cikinta, a kai matakin yankan shakku. Duk girman sana'a ko aiki, akwai wanda yake matakin ƙasa. KAI DAI KA RIƘE ABIN DA ZAI ZAME MAKA MAFITA A RAYUWA.
Kada ka manta!
Idan wani ya mallaki 'adaidaita sahu' 🛺 don dogara da kansa a yau, wani kamfanin ƙera su ya mallaka, wani kuma babban 'dealer' siyar da su ne. KOWA ABIN HANYAR ABINCINSA KENAN, kuma suna rayuwa cikin aminci da rufin asiri. Yadda MAI DIGIRI zai iya aiki a ƙasan maras DIGIRI a matsayin manager, accountant, staff... Haka MARAS DIGIRI zai yi aiki a ƙasan MAI DIGIRI a matsayin mai gadi, direba, cleaner, majinsa... Kowa abincinsa yake nema.
Ba wani abu da ya fi wani, fa ce wanda kai ya sama maka mafita a rayuwa, kai a karan kanka, ba abin da mutane suke confusion mutane sa shi ba.
✍️Aliyu M. Ahmad
16th Jumada I, 1446AH
18th November, 2024CE
#AliyuMAhmad #AliMotives #RayuwaDaNazari
0 Comments