Mu canja kanmu

Surutu ba zai canja ma a komai ba, face mu a karan kanmu mun canja.

Ƙarara a cikin Alƙur'ani Mai girma, cikin Arra'ad da Al-Anfal:, Ubangiji ﷻ yake cewa:

إن الله لا يغير ما بقوم حتى يغيروا ما بانفسهم

Ma'ana: "(Shi) Ubangiji ba ya sauya abin dake wata al'umma har sai sun canja abin dake kawunansu".

Ni da kai, ba za mu iya taruwa mu gyara dukkan 'yan Nijeriya ba, amma za mu iya gyara KANMU a ƊAIƊAIKU, sai kuma mu matsa wajen gyara waɗanda muke da iko a kansu na kusa, iyali, ƙanne... sai gyara maye kowa da ko'ina. Ba lallai ne mu iya canza halin mutane gaba ɗaya ko gwamnati ba, amma za mu iya fara wa da gyara kanmu, kuma daga nan mu rinƙa ƙoƙarin gyara waɗanda ke kusa da mu; waɗanda muke da tasiri a kansu, tare da sauƙe haƙƙoƙinsu dake kanmu.

Kai a karan kanka ka yi ƙoƙarin nema wa kanka mafita, saboda surutun gwamnati ta gaza, uncles ko wani boss naka ya ƙi taimaka maka ba zai canja komai a rayuwarka ba, face ƙara wa kanka damuwa.

Kai a karan kanka, ka kyautata ɗabi'unka da mu'amalarka da Ubangiji ﷻ da sauran bayinsa (mutane da sauran halittu). 

• Kana sauƙe nauyin iyalanka, yaranka a ofis ko kasuwa?  

Irin nauyi da yake kan shugaban ƙasa na nema wa 'yan ƙasa tsaro, tarbiyya, kare mutunci... da yake kansa, haka yake kai ma a kanka a cikin gidanka game da iyalanka.

• Kana cika alƙawarin da ka ɗauka na mutane? Wane irin riƙo kake yi wa amanar dake wuyanka?

Irin yadda 'yan siyasa ke alƙawari, da saɓawa; kai ma idan ka yi alƙawari ka gaza cikawa, duk layinku ɗaya, sai dai girma da nauyin alƙawari da saɓawar ya bambanta.

Kwanciyar hankali da ci gaba yin daidai ke tabbatar da su a kowacce al'umma, koda kuwa al'ummar ba ta MUSULUNCI ba ce, Kiristoci ne, ko masu bautar gumaka, ko ma marasa addini. CHINA, JAPAN, QATAR, FINLAND... misalai ne.

'Yan siyasa da shugabanninmu ba wasu baƙin mutane ne ba ne (daga wata ƙasa), mutane daga cikinmu suke samun dama, bal! Mune muke zaɓarsu da yatsunmu da bin son ranmu.

✍️ Aliyu M. Ahmad 
30th Rabi' II, 1446AH
2nd November, 2024CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments