Idan kana da dama, ka yi amfani da ita


Sai su ƙi yarda ko ma su ƙaryata mu...

...yanzu idan muka faɗa wa ƙannenmu, ba ma 'ya'yanmu ba; cewa, tsakanin 2000 - 2006 muna kashe ₦5 a kuɗin break na firamare. Mu sayi local snacks, ɗan malele, seasonal fruits da sauransu.

A tsakanin 2007 - 2010 kuwa, da ₦50 ne a sakandire, sai ka ci taliyar ₦20 ko ₦30, ka sha rake na ₦5 ko ₦10, ka ci wainar fulawa, mazarkwaila, local snacks... na sauran canji na ₦20.

Muna diploma tsakanin 2023 - 2015, a semester da kullum, a kowacce rana sai mun sha madara Peak ta gwangwani. A lokacin Peak tana tsakanin ₦100 - ₦120. A nan koyi cin Indomie idan ba kwai, ba za ta ciyu ba, lami ce!

Wannan dukka lissafin ƙasa da shekara 20 ne fa baya. Abubuwa da yawa sun sauya cikin sauri a yau
'.

Babban darasi da na ɗauka shi ne, idan ka sami damar aiwatar da wani a yau, ka ƙoƙarin cimma masa, kada ka jira wai sai abubuwa sun ƙara sauƙi. A Nijeriyar yau, ba a taɓa hawa sama an sauƙo ba, ko a dawo kamar baya.

Misali, tsakanin December, 2023 zuwa February, 2024 mun ɗan yi wani aiki. A farko December, 2023 mun sayi cement a ₦5,000 per bag. A January, 2024 ya kai ₦7k+, a February, 2024 sai da ya haura ₦8k+.

Saboda kai, kana da wani buri, ba wani abu da zai sauƙo. Ko dai ka ƙoƙarta ka yi yadda za ka iya, ko kuma ƙara azamar nema don fitting buƙatunka, amma dai kada ka jira wani lokacin sauƙi don za ka yi aure, ko gina gida, ko buɗe wata sana'a, ko cimma wani buri dake buƙatar kuɗi.

✍️Aliyu M. Ahmad
8th Jumada I, 1446 AH
10th November, 2024 CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments