Waye zai sanya ka farin ciki?


Akwai mutum da zai ba ka farin ciki ko baƙin ciki? BABU, sai wanda ka zaɓa. Sai dai aiyukan wasu za su iya sanya farin ciki ko baƙin ciki, shi ma yana da alaƙa da wasu abubuwa (factors), mafi rinjaye ra'ayi da halinka.

A nazariyyar halayya (psychology) akwai wani abu da ake ƙira da 'attitudinal effect', ma'ana yanayin da halayyar mutum ga abu ke tasiri a ta mu rayuwar. Halayya da tunanika ga wasu za ta iya zama 'negative' ko 'positive'.

Misali, 

Budurwa ce tana da masoya mutum 2, 'A' da 'B'; amma ta fi son 'B'. 

Idan da 'A' zai ƙira ra 5x a rana, za ta ɗaga tana yamutsa fuska, wataƙila har ta ƙira shi da 'ɗan wahala' (duk da halin kulawa da yake ba ta) saboda zuciyarta ba a kansa take ba.

Amma da 'B' zai ƙira sau 1, tana murna da rawar jiki za ta amsa wayarsa.

A wajenta kyauta r₦1000 ta 'B', za ta fi faranta mata rai fiye fa ₦10,000 ta 'A'. Da 'A' zai yi mata laifi 1, za ta kwarmata, amma da 'B' ne zai yi mata 1000, za ta haƙuri da shi, ba ta ma so wani ya ji.

A hakan nan a wajen fahimtar zance, idan 'attitude' naka ga 'X' ya fi karkata, duk abin da 'X' ya faɗa koda kuskure ne sai ka yi ƙoƙarin juya shi da kyakkyawar fuska. Amma 'Y' da kake adawa da shi, ko mai kyau ya faɗa, sai ka ga abun nan a baibai. Yadda muke mu'amalarta abokan adawar siyasa da malamai misali ne.

Da zarar ya zama farin cikinka yana da alaƙa da wani ne, ka hana kanka nutsuwa, muryar wani ne zai sanya maka farin ciki, za ka iya simpanci kashe kuɗinka don farantawa wanda ba ya ƙaunarka, ko zubar da da mutuncinka... kana cikin jinya ne ba soyayya ba (emotional depedence/codependency), a likitance kuma kana buƙatar ganin likita.

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments