Me Zan Bibiya a Social Media?


Ka gane me kake so a social media,
Mene ne ya yi daidai da manufarka a rayuwa.
Abubuwa da yawa ba su da alaƙa da kai, ka bar sum

Kada ka riƙa barin kowanne yayi da tarkace yana shiga tunaninka. Ka sani! Tunani kamar abinci ne a jiki. Wani zai gina ka, wani kwa zai ɓata maka ciki, har ya saka ka jinya.

Kai ɗan makaranta ne (ɗalibi) ka bibiyi masu posting kan fannin da kake karanta LAW, MEDICINE, SCIENCES, LANGUAGE, IT, SOCIAL SCIENCES,.MANAGEMENTS... duk akwai su, masu contents na Turanci da Hausa, rubutu da bidiyo.

Kai ɗan kasuwa ne ko ma'aikaci, ko wani skills; ka riƙa bibiya masu posting kan yadda za ka bunƙasa kasuwanci, kwarewarka a kasuwaci, content creation, graphic design... ga su nan birjik, Hausa da Turanci, bidiyo da rubutu.

Ka riƙa sanin wasu 'postings' ba ka da alaƙa da su kwata-kwata, wasu kuma sun ɗan dangance ka. Sanin wannan zai sa ka daina damuwa da wasu al'amuran.

Misali, Idan aka yi magana kan falalar Turanci don neman abinci, kai kuwa ko bokon ma ba ka yi mai zurfi ba, kasuwanci kake kana juya miliyoyi. Kada ka damu, irin wannan post ba don kai aka yi ba, na 'YAN LABOUR MARKET ne. Kada kuma ka shiga kushe mutane, saboda ba su zama ire-irenka ba.

Sai kuma ka kiyaye ɗebo tarkacen tunanin komai ka gani wani ya yi nasara ka ce kai ma kai ma za ka gwada. Yau ka kama wannan, gobe ka saki, ka ƙara kama wani... Sai ka dawo ka fara jin haushin kanka saboda ka kasa kataɓus. Ba lalle ne komai wani ya yi nasara kai ma za ka yi ba, ka koma ka ƙara karantar kanka, baiwarka, manufarka, ka gina skills da consistency. Wani connection ya kai shi ga nasara, wani kuma personal brand. Ka yi kataɓus, ka bar wa Allah sauran.

✍️Aliyu M. Ahmad
25th Jumada I, 1446 AH
27th November, 2024 CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments