Addiction


Wani zai ce:

Ka daina shaye-shaye,
Ka daina neman mata (z*na),
Kul kake kallo b*tsa,
Ka musulunta,
Ka dawo sunnah,
Ka daina sata...

Wasu mutane suna zaton don kana wani abu na RASHIN KIRKI ko SAƁO (KAWAI DA FURICIN BAKI 🗣️) don ka ce ya daina, kada ya yi, kawai sai ya daina? 

An ce maka halayya riga ce da za ka iya cirewa da canja a lokaci 1? Yanzu take ⏰? 

Eh, da furicin baki ake fara da'awa, nasiha... amma WANI LOKACIN, MUNE MUKE ƘARA TUNZURA WASU, SU SAKE MAƘALEWA BA DAIDAI BA, saboda rashin sanin yadda motsin zuciya yake.

Wani abu da yake ba mu wahala a rayuwa shi ne, rashin fahimtar MOTSIN ZUCIYA. Halayya ba riga 👕 ba ce da za ka iya cirewa a lokaci guda, domin tana da tushe a zuciya 🫀da motsinta, kuma tana da tasiri daga abubuwan da mutum ya saba da su da kuma yanayin rayuwarsa. A matsayinmu na mutane, canjin halayya yana buƙatar lokaci da himma.

Misali:

Abokinka ko ɗanka yana shaye-shaye 💊💉🍻, don kana mahaifi ko aboki, kana da ikon bada shi shawara, amma ba ka da ƙarfin tursasa shi ya daina aikata ba daidai ba. Saboda, ko kai ne kake shaye-shaye, baka da ikon hana kanka cikin sauƙi (sai dai idan Allah ne ya nufe ka da shiriya a kusa), saboda sabo (addiction). Kayan mayen ke sarrafa su, ba su ke sarrafa kayan mayen ba. Ga wanda ya yi nisa (addict), ba watsar da shi za a yi ba, don kamar mai jinya ne, akwai matakan daidaita halayya na 'addiction recovery' ya kamata a raka shi ciki.

Ka san dalili?

ADDICTION 👹, ma'ana yawan maimaita abu koda zuciyar mutum ba ta so. Addiction yana fara wa daga lokacin da mutum yake wani aiki yana jin daɗi, a hankali sai ƙwaƙwalwarsa ta fara fitar da sinadaran 'DOPAMINE' a wasu sassa na cikin kwakwalwa (substantia nigra da ventral tegmental).

Wannan sinadrin shi zai riƙa motsa wa mutum sha'awar shan kayan maye (SUD), ko neman jin daɗi na sha'awa (kamar kallon b*tsa, z*na, luwaɗi/maɗ*go), caca, ADHD (mesolimbic), sanya tunane-tunane (mesocortic)... koda mutun ba ya so, sai yi kallon b*tsa, ko wasa da hannu, ko shaye-shayensa sannan ya iya samun nutsuwa.

YADDA KA TARA WA KANKA SINADARAN "DOPAMINE" A HANKALI, A HANKALI, HAKA RAGE SU MA SAI A HANKALI, A HANKALI. Ni da kai kuma, ba mu fi ƙarfin faɗawa cikin wannan halin ba, sai dai ƙoƙarin kiyayewa, Allah ya kiyaye mu!

Mafi ƙaranci kwanakin da mutum zai ɗauka don rage DOPAMINE sune kwanaki 30 ba tare da motsa waɗancan sinadan ba 'detox' (shi ma ya danganta da ƙarfin shaƙuwa). Yana daga cikin hikimar Ubangiji ﷻ wajabta wa bayi azumin kwana 29/30 a shekara don su daidaita halayayyarsu, a guje wa saɓo, da ginuwa kan aiyukan ɗa'a. Manzon Allah ﷺ kuma ya umarci matasa da yin aure, don biyan buƙata ko yin azumi domin kamewa. Likitoci ma suna bayar da "antipsychotics" da suka dace da mutum don rage wannan sinadarin.

Koda Musulunci ya zo, bai hana SHAN GIYA a lokaci guda ba, sai da aka ɗora halayyar mashaya a mataki 4:

1. An fara nuna illar (Baƙara, aya ta 219),
2. Sai kuma aka hana shan giya a lokacin ibada, i.e. salla (Nisa'i aya ta 43),
3. Sai aka hana shan giya gaba ɗaya (Ma'ida, aya ta 90)
4. Sai kuma aka sanya hukuncin bulala 80 ga wanda aka kama ya sha giya (Muslim, 2003).

• ABU NA BIYU:

Ba lokaci guda kawai za ka ce wa mutum ya MUSULUNTA ya bar nasa addini ya kama naka ba. Ko ya bar tasa ƙungiyar addini ko ra'ayi da ya taso ya ga ana yi a gidansu ya kama taka kungiyar ko fahimtar ba. Tunani, ra'ayi da yarda wasu ababe ne da zuciya ke ginuwa a kai, kuma suna da matuƙar wahala rsauyawa (sai ga wanda Allah ya sauƙaƙawa).

Wani lokaci, tun kafin ka faɗa wa mutum gaskiyar da kake son ya ɗauka ka tunzura shi (ka zage shi, ka muzanta shi), har ya ji ya tsane ka, ta ya zai karɓi gaskiyarka? Kai a zatonka kana faɗar gaskiya ko ba daɗi. BA KA TUNA FAƊI ALLAH A NAHL (aya ta 125) BA? ادع إلى سبيل ربك بالحكمة والموعظة الحسنة. 

Me Ubangiji ﷻ ya ƙara da faɗin cewa "إنك لا تهدي من أحببت ولكن الله يهدي من يشاء" a cikin Ƙasas aya ta 56.

Abu ne mai sauƙi, mutum ya faɗa aiyukan assha, amma abu ne mai wahala ya iya cire kansa. Sannan riƙe wata aƙida ko ra'ayi kuma da yake tushe daga asali (iyaye ko muhalli), canja su na buƙatar gamsuwa. Kai dai ka godewa Allah da ka sami addini da araha, kuma ba ka haɗu da wasu halaye banza masu naci ba (addicts). Wani lokaci, ba za ka fahimci girman halayya ba, sai ka tsinci kanka a ciki. 

✍️Aliyu M. Ahmad
27th Jumada I, 1446 AH
29th November, 2024CE

#AliMotives #RayuwaDaNazari #AliyuMAhmad

Post a Comment

0 Comments