Ƙanwata



A lokacin da kike kan ganiyar budurci, yarinya fresh, sabuwa gal, mazaje da yawa za su fara approaching neman soyayya dake.

A lokacin ke kuma kanki zai ɗau zafi, kina jin kin isa, kina da farin jini. Duk idan kika je, kasuwa, makaranta, unguwa... sai wani ya tsayar dake. Waya daga kin ajiye wannan, wani zai ƙira, SMS, chattings... KINA JI A KANKI, ai kina da zaɓi da yawa. Kina jin, kina da kyau, kina da farin jini, kina da... Wannan lokacin ake ƙira da 'PRIME/BLOOM OF YOUTH'.

A wannan lokacin yana da kyau ki nutsu. Waɗannan mazajen/samari, da za ki fara cewa, an ce ka fito, ka turo, ka zo ku yi magana da Baba... za su fara zarewa one-by-one. Sai ki gane, burge su kike yi, ba wai aurenki za su yi, ko za su iya ba.

Ke kuma wataƙila a lokacin kin ma waɗanda suke miki kulawa da yawa wulaƙanci. Ko ƙori waɗanda suka shirya aurenki da gaske, saboda kina tunanin kina da zaɓi da yawa. Idan ma kin rasa Malam, kina da Engineer, ko Likita.

Ɗaiɗaikun 'yan mata ke samun gatan tsarewa daga iyayensu mata, na hana su bibiye da ruwan ido, har Allah ya kawo na gaske, maimakon kule-kule da ɓata lokaci. 

Sai kin haɗa da addu'a da takatsantsan, kada ki bar gayu su ɓata miki lokaci. Kin yar na gaske, kin kama gaibu, a lokacin da za ki gane gayun da kike biya wa ba aurenki za su yi ba, lokacin kin waiwayo masu son ki kuma da gaske da son aure, su kuma sun yi nisa, har sun sake wani zaɓin.

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments