Matasa dai ake cuta da SUNAN MOTIVATION, duk an rikita musu tunani. WASU BA 'MOTIVATION' SUKE BA, damuwa suke ƙara ɗorawa da jin ƙasƙanci suke sakawa mutane.
Mai son ya 'motivating' (zaburar da) mutane, sai yana kula da kalmominsa, domin tasirinsu ga mai karatu ko sauraro, koda da wasa kake, wasu da gaske suna shiga cikin damuwa da jin ƙasƙanci (inferioty complex).
1. Idan Ubangiji ya ma luɗufi ka yi wata nasara cikin matsakaitan shekaru, kar ka furta ga wanda ya kai irin shekarunka, bai samu irin nasararka ba a matsayin maras nasara, kai wayonka ne ya sa ka yi nasarar? Harland Sanders mai kamfanin 'KFC' ya yi nasara kafa kafaninsa na KFC ya ɗan shekaru 74, ya mutu a ɗan shekaru 90.
Amma Gimbiya Charlotte, ƴar shekara 7 da haihuwa, ta samu gadon dala biliyan 5 (takwancin ₦11.3 trillion a yau November, 2024) daga gadon Queen Elizabeth II. Ai! NEMA NE NAMU, ARZIƘI NA ALLAH NE.
2. Don ka yi aure a 'yan shekaru, ko kana da mata 2, ko 3... ba 'motivation' ba ne nunawa wanda bai da aure, ko kafi shi yawan mataye (da 2, 3).... cewa, bai more rayuwa ba, FARIYA CE! GORI NE! Wani sai ya ji damuwa, don an ce baya morewa, bal, wani maras aure ma, yafi mai auren kame kai, da kwanciyyar hankali.
Akwai manyan mutane da har duniya ta naɗe, tasirinsu ba zai gushe ba, sun mutu ba su yi aure ba, cikin har da annabawan Allah, sahabbai, salihan bayi, manyan masana kimiyya... hakan ba zai shafi shigarsu rahamar Ubangiji ba.
Misali, Karimah bint Ahmad Al Marwaziyyah (Ummul Kiram) ta rasu 465AH ba tare da ta yi aure ba, Annabin Allah Yahaya عليه السلام, Imam Attabari, Zamakhshari, Annawawi, Ibn Taymiyya رحمهم الله... a kimiyya: Isaac Newton... da sauransu, duk sun koma ga Allah ba tare sun ƙulla alaƙar auratayya ba.
3. Idan kanka na ja a makaranta (kana da ƙoƙari), ba shi ke nuna kana da nasara bayan makaranta ba, kowa da irin baiwa da kaifin kwakwalwa da Allah ya ba shi; wani a karatu, wani a kasuwa, wani baiwar sana'a, wani a siyasa... sai ka fita da 1st/2nd Class, mai Third Class ya ɗauke ka aiki a kamfaninsa, ko Secretary/P.A. a ofishinsa.
Elon Musk (mai SpaceX da Tesla), wanda yafi kowa kuɗi a duniyar yau, yana yawan nanatawa, "BAN JE HAVARD UNIVERSITY BA, AMMA NA YI HAYAR WAƊANDA SUKA JE 'HAVARD' SUNA AIKI A ƘARKASHINA, INA BIYANSU."
4. Don kana jin kanka a matsayin wanda ya samu shiriya, ba 'motivation' ba ne nesanta wasu daga rahamar Ubangiji. Ta iyu wasu a ɓoye, tsakaninsu da Ubangiji, aikin taimako da jinƙansu ya jawo musu rahamar Allah. Cikin hikima ake kwaɗaitarwa zuwa ga aiyukan alheri.
Motivation shi ne, ka sanya wani jin kwarin gwuiwar zai yi nasara, ba kana kwatanta kanka a matsayin mai nasara ba (saboda ka yi aure, ko tara dukiya ko ilimi, ko samun wata dama, ko yawan ibada ba), har mai bibiyarka ko sauraronka yana kallon, kai ka wuce shi nasara, ya ji damuwa a tattare da shi (wannan na haifar da 'inferiority complex' a tunani). Maganar gaskiya ba motivation ba ne wannan. Kai kuma fariya kake, ba motivation ba.
✍️Aliyu M. Ahmad
15th Rabi'ul Thani, 1442AH
10th November, 2022CE
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives
0 Comments