Rayuwa ta Sauya


Rayuwa fa ta sauya, 
Dole ne mu ma mu sauya.
Idan ba ka yi hankali ba, 
Mutane za su koya maka hankali.

1️⃣. Babban yaya ne a gida, bayan mahaifinsu ya rasu (mutu) zai ɗauki ɗawainiyyar ƙannensa, karatunsu, cinsu, shansu, suturarsu... har su girma su zama mutane. Bayan ya ja shekaru, shi ma ya rasu (mutu), ƙannen san nan da ya mayar mutane, za su rarraba 'ya'yansa don su riƙe, kamar yadda shi ma ya riƙe su suka zama mutane.

Amma abin mamaki, sai ka ga yaran nan sun tagaiyara, sun zama 'ya'yan bora a gida. Matan gidan suna bambanta ta su da 'ya'yan da suka haifa, yara su zama kamar wasu leburori a cikin gida.

Dole ne yanzu ka koyar da 'ya'yanka SANA'A kamar yadda kake koyar da su ILIMI da TARBIYYA. Ka nema wa matarka abin da za ta iya dogara da kanta, kada ka ce dole kowa sai ya jingina da kai, watarana ba ka nan.

Ko me ya sa wasu matan ba sa sanin ƙimar haihuwa sai iya waɗanda suka haifa (kaɗai)? Ya za ki ji idan an ce ke ce kika mutu, aka yi wa 'ya'yanki irin wannan riƙon? Idan akwai wani mummunar ɗabi'a da nake tsoro game da ɗan Adam, ba ta wuce 'sociopath' da 'narcissism'.

2️⃣. A yau akwai mutumin da yana rufin asiri sosai, amma ba shi da ₦1k a aljihunsa ko a banki, saboda duk kuɗin suna hannun mutane (bashi), shi ma sai ya ci bashi zai biya wasu buƙatunsa.

3️⃣. Dole sai an ƙara azamar nema, an kuma saita yadda za riƙa kashe kuɗaɗe ba kamar a baya ba. Duk abu da ba dole ba, a haƙura da shi. Duk wanda zai ɗora maka nauyi da ba za ka iya ɗauka, ka ce "a'a!" Ba tare da ka yi shakka ba.

Duk hidimar da za ka yi 'yan uwa da iyali, da zarar ba ka da shi babu mai yi maka uzuri, wani ma sai ya ce, "me ya sa ba ka tattali da adani" kamar yadda aka bayyana a hoton ƙasa 👇.  

TAKE YOUR FINANCIAL LIFE SERIOUSLY. MONEY IS A DEFENSE TO A LOT OF CHALLENGES.

✍️Aliyu M. Ahmad
5th Rabiʻ II, 1446 AH
8th October, 2024 CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments