Focus: Mayar da hankali


A wata 2 (August da September) da na daina social media (detoxification), na cimma abin da na kasa cimma a wata 7 farkon 2024.

Duk abin da yake da muhimmanci, ka ba shi lokaci, ka yi da gaske, kai ke da riba.

Social media tana saka damuwa da É“acin rai, ka ji labarin wasu da bai shafe ka ba yana É—aga maka hankali, har ana musu da jayayya da cin mutuncin juna, a kan me?

Social media tana saka jinya, wasu masu amfani da social media fiye da ƙima majinyata ne alhanin ba su sani ba, ga FOMO, son shahara, damuwa da abin da bai shafe ka ba.

Social media tana cinye lokaci, aikin da za ka kammala a 30mins, sai ya ɗauke ka 2hrs saboda social media. 1hr 30mins ya tafi a scrolling feeds, productivity naka yana yin ƙasa.

Ka san yanzu ko a wasu wuraren É—aukar aiyuka bayan an duba takardunka, ka yi bayanin kanka, ana kuma duba social media handles naka domin a Æ™ara tabbatar da kai waye, ya kake bayyana tunaninka ma duniya (social media)? Su waye abokanka? WaÉ—anne shafuka kake bibiya? 

Social media tana da alheri! Mu yi amfani da social media don gina kanmu, kada mu yarda ta mallake mu mu rasa kanmu da wayar da muka sa kuÉ—i muka siya, da data da muka siya.

Fatan alheri.

- Aliyu M. Ahmad
1st October, 2024

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments